Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo mai fuskoki da dama yana matukar son zama shugaban kasar Amurka
2020-08-13 20:48:22        cri

Kwanan baya, Mark Brzezinski, dan shahararren ma'aikacin huldar jakadancin Amurka, ya shaidawa manema labarai na CMG cewa, kudi da neman kuri'u, sun zama tushen siyasar Amurka, kuma wasu 'yan siyasa masu neman riba sun kutsa kai cikin gwamnati yadda suka ga dama, cikin su hadda Mike Pompeo wanda ya yi kaurin suna a wannan bangare.

A matsayi wani ma'aikacin diplomasiyya maras ci gaba, a tsawo shekaru biyu da ya yi yana aiki, Mike Pompeo na da fuskoki da dama, inda ya dage wajen dora laifi kan sauran kasashe, game da gaza daukar matakan da suka dace don yakar COVID-19 a Amurka, da kuma illata hadin kan da aka samu a wannan fanni, lamarin da ya jefe jama'ar kasar Amurka cikin wani hali mai hadari.

Game da zanga-zanga da aka yi dake da alaka da adawa da nuna bambancin launin fata, ya yi kamar ba ya ji ko ba shi da masaniya, ya ci gaba da goyon bayan tsarin daukar matsayi biyu salon Amurka, bisa ra'ayin rashin lura. Ban da wannan kuma, ya dauki matakin matsawa kasar Sin lamba, don dora laifi kan ta, yayin da yake fuskantar rikicin al'umma cikin kasarsa. Ta wannan hanyar ne kuma yake yunkurin neman kuri'u ga bangaren da yake goyon baya.

Mike Pompeo mai fuskoki da dama, ya yi biris da nauyin dake wuyansa, a matsayin wani ma'aikacin diplomasiyya, ya kuma bar mutunci da muradun kasarsa, da na jama'a a baya, don cimma bukatar zama shugaban koli a kasar a nan gaba.

Gaza sauke nauyin dake wuyansa, da kuma neman moriya ta hanyoyi marasa kyau, da dai sauransu laifuffuka, dukkansu alamu ne na Mike Pompeo, amma abun tambaya a nan shi ne, me ya ba shi da karfin gwiwar yin hakan? Dalili shi ne, gaggauta yiwa shugabannin kasar kanzagi. Jaridar Washington Post ta fadi gaskiya da ta ce, sharudda mafi muhimmanci don shiga jikin shugabannin gwamnati a wannan karo su ne nuna rashin kunya. A wannan fanni kuwa, babu wanda zai zarce Mike Pompeo.

A wani bangare na daban kuma, Mike Pompeo ya dauki kwararan matakai kan batun dangantakar dake tsakaninsa da yankin gabas ta tsakiya, da Korea ta arewa. Har ma ya tilastawa gwamnatin kasar biyan bukatunsa ta hanyar nuna rashin imani. Kafar CNN ta taba ba da labarin cewa, Mike Pompeo shi ne mutum daya tilo da ya kitsa shirin kashe babban hafsan sojin kasar Iran, wanda hakan mataki ne da ya sabawa babbar manufar diplomasiyya da gwamnatin Amurka ke dauka.

Idan masu neman riba kamar Mike Pompeo sun jagoranci manufofi dake da alaka da kasar Sin, zuwa wata hanya ta kuskure, to lallai Amurkawa ne za su ji a jikin su. Yayin da shi kuma Mike Pompeo zai kafa mummunan tarihi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China