Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban zirga-zirga ya taimakawa 'yan kabilar Tibet fita daga kangin talauci
2020-08-13 13:59:10        cri

Kamar yadda a kan ce, idan ana son samun wadata, na farko shi ne a shimfida hanya. Wannan karin magana ya jaddada muhimmancin zirga-zirga ga bunkasar tattalin arziki. A yayin da kasar Sin ke aiwatar da shirin raya kasa na 13 na shekaru biyar daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, ta kara zuba kudade a fannin zirga-zirga a jihar Tibet da sauran wurare, lamarin da ya taimaka wa al'umma 'yan kabilar Tibet wajen fita daga kangin talauci da ma samun wadata.

Lv Yida, wanda ke aiki a cibiyar aikin ceto a kan teku ta kasar Sin a karkashin jagorancin ma'aikatar zirga-zirgar kasar, ya taba rike mukamin shugaban kula da aikin fama da talauci a kauyen Rela na gundumar Heishui da ke lardin Sichuan daga watan Satumba na shekarar 2017 zuwa watan Satumba na shekarar 2019. A tsawon wa'adin aikinsa, an shimfida hanyoyi na tsawon kilomita 6.9 a kauyuka, har ma motocin fasinja na iya shiga da fita.

"Ci gaban zirga-zirga ya sa mazauna kauyen kara samun damammaki na zuwa garuruwa don cin rani. Ban da wannan kuma an kara samun damar raya aiki. A kuma samu injunan ayyukan gona da kayayyakin kiwon dabbobi da kayayyakin samarwa da fasahohin shuke-shuke da kiwon dabbobi daga sauran wurare cikin sauki, lamarin da ya taimaka sosai ga ci gaban sana'o'in kiwon kaji da kudan zuma a wurin."

A ganin Lv Yida, a da, idan mazauna kauyen Rela, suna so fita waje, suna taka sayyada ne cikin zafin rana da ruwan sama, amma yanzu da zarar sun fita daga gidajensu, akwai hanya mai inganci, su kuma shiga motar fasinja. Amma abu mai muhimmanci shi ne, kyautatuwar muhimman ababen more rayuwa musamman ma zirga-zirga ta canja tunanin mazauna kauyen a fannin rayuwarsu.

"Bayan da mazauna wurin suka yi cudanya da dangogi da abokansu da ma masu yawon shakatawa, kan su ya kara wayewa. Musamman ma matasa, sun fi son fita waje don bude ido da ma cin rani. Ban da wannan kuma, dimbin dalibai sun bayyana aniyarsu ta komawa kauyen bayan sun gama karatu a jami'a don hada kai tare da 'yan kauyensu wajen raya aiki da ma samun wadata tare."

Sakamakon wasu dalilai na halittu da na tarihi, jihar Tibet ta taba kasance yankin da aka fi samun yawan mutane masu fama da kangin talauci, kana mafi shan wahalar fita daga fatara. A yayin da kasar Sin ke aiwatar da shirin raya kasa na 13 na shekaru biyar daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, Ana ta kara zuwa jari wajen shimfida hanyoyin motocin jihar Tibet, lamarin da ya sa hanyoyin jihar samun kyautatuwa sosai. Xu Wenqiang, shugaban hukumar zirga-zirga ta jihar Tibet ya furta cewa,

"Yanzu haka, akwai hanyoyin mota masu tsawon kimanin kilomita dubu 104.5 a fadin jihar. Ingancin hanyar mota tsakanin Qinghai da Tibet mai tsawon kilomita 1140 ya kai matsayi na biyu bisa ma'aunin hanyoyin mota na kasar Sin. Ban da wannan kuma, muna shimfida hanya mai lamba 345 tsakanin Qinghai da Tibet, da hanya mai lamba 216 tsakanin Xinjiang da Tibet, ana kuma sa ran za a fara amfani da su a karshen wannan shekarar da muke ciki. Ya zuwa yanzu, an riga an kafa cikakken tsarin zirga-zirga a jihar Tibet. A nan gaba kuma, masu sha'awar zuwa Tibet yawon bude ido da ma al'ummar jihar za su samu sauki da ma tsaro sosai a fannin tafiye-tafiye."

Xu Wenqiang ya kuma nuna cewa, a kokarin da ake na warware matsalar zirga-zirga da al'ummar jihar Tibet ke fuskanta, gwamnatin jihar ta mai da hankali kan shimfida hanyoyi zuwa kauyuka da garuruwa na jihar. A cikin shekaru hudu da suka gabata, jihar ta kebe kudi Yuan biliyan 94.16 wajen gudanar da ayyukan shimfida hanya 3123 a yankunan karkara, da gyara hanyoyi da suka kai tsawon kimanin kilomita dubu 38.2.

Yanzu haka, akwai motoci na kaiwa da dawowa a hanyoyin da ke yankunan gona da kiwon dabbobi, wadanda suka taimaka wajen ci gaban sana'o'i daban daban. Ba ma kawai al'umma 'yan kabilar Tibet sun samu hanyoyi masu inganci da sabbin motoci ba, har ma sun kara jin dadin zaman rayuwarsu mai cike da wadata.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China