2020-08-12 13:26:57 cri |
Ya zuwa karshen shekarar bara, adadin tsoffi masu shekaru sama da 60 dake birnin Shanghai ya kai kaso 35.2 bisa dari na al'ummar birnin, adadin mafi yawa a fadin kasar Sin, kana adadin tsoffi wadanda shekarunsu suka kai sama da 80 a birnin ya kai kaso 15.8 na tsoffi masu shekaru sama da 60, to, yadda ake kula da su ya jawo hankalin daukacin tsoffin dake rayuwa a birnin.
A cibiyar samar da hidima ga tsoffi a cikin unguwar dake kan titin Hongqiao na yankin Changning na birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, a kan fara samar da abincin rana ga tsoffi da karfe goma da rabi na safe, gyautuma Chen mai shekarun 79 da haihuwa tana zama a kusa da cibiyar ce, a don haka ta kan ci abinci a nan ko wace rana, ta gaya mana cewa, tana son cin abinci a nan saboda bata bukata ta dafa abinci a gida da kanta, kuma abincin da ake samarwa a nan babu tsada.
Ban da cin abinci sau uku a ko wace rana, ana kuma iya duba lafiyar tsoffin dake zama a kusa da cibiyar mai fadin muraba'in mita 3072 da sayen magani, su kuma karata littafi, da motsa jiki a ciki, kana su kan shirya ayyuka iri daban daban domin nishadi.
A bene na uku na cibiyar, an ga tsoffi sama da goma suna motsa jiki ko karanta littafi, wasu kuwa suna yin atisayen samar da kayayyakin fasaha bisa taimakon ma'aikatan cibiyar, gyautuma Gu mai shekarun 72 da haihuwa tana shafi farin fenti a jikin wani kayan wasa mai siffar yaro, makasudin yin haka shi ne domin kyautata amfanin hannu, ta gaya mana cewa, "Ina zuwa nan ko wace rana, saboda ni kadai nake zama a gida, a don haka na kan zo nan domin halartar ayyukan da aka shirya har ma na motsa jikina, ban a iya daukar kaya da hannu, kafafuna ma ba su da karfi, shi ya sa na kan zo nan don na motsa jiki ta hanyar yin amfani da kayayyakin motsa jiki na zamanin da aka samar a nan, yanzu na sami sauki, ina jin dadi a nan, wurin ya zama tamkar gidana."
Hakika dalilin da ya sa tsoffi suke son zuwa nan cin abinci ko motsa jiki shi ne domin ba ma kawai abincin cibiyar ba su da tsada ba, har ma ma'aikatan cibiyar suna samar da hidimomi masu inganci gare su, kana abu mafi muhinmnanc shi ne cibiyar tana cikin unguwar, inda take kusa da gidajen tsoffin.
Domin samar da hidima mai inganci ga tsoffi, hukumar kula da harkokin jama'a ta birnin Shanghai ta yi kokari matuka, mataimakiyar shugaban hukumar kula da harkokin jama'a ta birnin Shanghai Jiang Lei ta bayyana cewa, "An lura cewa, yawancin tsoffi ba su son zuwa cibiyar kula da tsoffin da aka gina a nesa da wurin da suka saba, shi ya sa hukumar kula da harkokin jama'a ta birnin Shanghai ta fi mai da hankali kan aikin samar da hidima ga tsoffi a cikin unguwanni, dalili shi ne, a kafa cibiyar kula da tsoffi a cikin unguwanni, inda take kusa da gidajen tsoffin, ta haka tsoffi suna iya jin dadin hidimomin da ake samarwa ba tare da barin muhallin da suka saba ba."
Hadaddiyar cibiyar kula da tsoffin da aka kafa a kan titin Hongqiao na yankin Changning na birnin Shanghai tana da benaye uku, akwai wurin samar da abinci da wurin samar da hidimar kiwon lafiya da wurin jinya da sauransu a bene na farko, a bene na biyu kuwa, akwai wurin kula da tsoffi na Hongqiao na birnin Shanghai, inda aka samar da gadajen kwanciya da dama ga masu bukata, a bene na uku, an samar da hidimomi iri daban daban, alal misali kula da tsoffi da rana, da taimakawa tsoffi motsa jiki, ko yin wanka.
Game da hidimomin da ake samarwa a cikin cibiyar, shugabar hukumar kula da harkokin jama'a ta birnin Shanghai Zhang Wei ta gaya mana cewa, an yi cikakken bincike kan bukatun tsoffi kafin aka gina cibiyar, tana mai cewa, "Mun gudanar da bincike kan bukatun tsoffin dake rayuwa a yankin Changning a shekarar 2018, daga baya mun tsara shirin aiki kan bukatun tsoffin, yanzu haka muna kokarin kyautata aikinmu na samar da hidimomi ga tsoffin."
A halin yanzu an riga an kafa cibiyoyin samar da hidima ga tsoffi irin wannan guda 268 a daukacin titunan fadin birnin na Shanghai, mataimakiyar shugaban hukumar kula da harkokin jama'a ta birnin Jiang Lei ta bayyana cewa, nan da shekarar 2022, adadin cibiyoyin zai kai sama da 400.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China