Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabshin Nijeriya
2020-08-11 16:38:17        cri

Batun tsaron al'umma da dukiyoyinsu, muhimmin batu ne da ya rataya akan kowacce gwamnatin da ta san ya kamata. Duk ci gaban kasa da karfin tattalin arzikinta, idan babu tsaro, to al'ummarta da ita kanta ba za su taba zama cikin kwanciyar hankali ba.

Rikici da hare-haren kungiyar Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa, wanda ya fi kamari a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, batu ne da ya dade yana ci wa al'ummar kasar tuwo a kwarya, inda suke ganin kamar an gaza wajen murkushe su, lamarin da ya kai su ga kira da a sauya shugabannin hukumomin tsaron kasar, ganin cewa sun kai kimanin shekaru biyar a kan mukamansu.

Ana iya cewa bayan gwamnatin kasar mai ci ta kama aiki, an samu ingantuwar yanayin tsaro sosai, inda mayakan kungiyar suka daina kai hare-hare kamar yadda suka yi a baya. Ba shakka an karya lagonsu a wancan lokaci, amma kuma a baya-bayan nan, kungiyar ta dauki sabon salon kai hare-hare kamar yadda ta saba, kan mutane masu rauni da jami'an tsaro da kuma sace mutane da neman kudin fansa.

Wannan sabon salo da ya harzuka jama'a ne ya kai ga gwamnonin jihohin yankin biyar da suka hada da Adamawa da Bauchi da Borno da Taraba da Yobe, yin tattaki zuwa fadar shugaban kasar a jiya Litinin, domin jan hankalinsa da kuma shugabannin tsaro game da yanayin da ake ciki a jihohinsu. Kamar yadda a kullum ake cewa, nasara ba ta samuwa sai da hadin kai. Duk da bambancin jam'iyyar siyasa dake tsakanin gwamnonin, sun hada hannu domin ganin sun tunkari matsalar da ta addabi al'ummarsu.

Yayin taron na jiya, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya lashi takobin kawo karshen matsalar a yankin da ma kasar baki daya, inda a cewarsa, gwamnati ta sayi sabbin kayayyakin aiki tare da daukar sabbin matakai, yana mai cewa, nan bada dadewa ba, za a shawo kan matsalar.

Irin wannan bayani da alkawari, zai kara ba al'umma kwarin gwiwar yin ammana da gwamnati, domin suna bukatar sanin inda aka kwana dangane da batutuwan da suka shafesu, musammam batun tsaro da yaki ci yaki cinyewa. Bisa la'akari da yadda suke ganin gazawar gwamnatin, sanar da su wainar da ake toyawa ka iya kwantar musu da hankali da karfafa musu gwiwar bada tasu gudunmawa domin a gudu tare a tsira tare. Yadda daukacin lokaci gwamnatin ke yin gum, na sanya kokonto cikin zukatan jama'a, su ga kamar an yi biris da matsalolinsu, ko da kuwa a hakikanin gaskiya, tana iya bakin kokarinta.

Kamar yadda shugaba Buhari ya ce ana daukar sabbin dabaru, a gaskiya lokaci ya yi da ya kamata jami'an tsaro su sauya salonsu da dabaru. Hausawa kan ce idan kidi ya sauya, rawa ma sai ya sauya. Tabbatar da cimma nasara a fannin tsaro na bukatar sauya dabaru akai-akai domin gudun mayar da hannun agogo baya. Dole ne a kullum dabarun jami'an tsaro su kasance sabbi domin shammatar abokan gaba da kuma ci gaba da yin tasiri, ta yadda za a samu dauwamammiyar nasara.

Bai kamata gwiwarsu ta rika yin sanyi bayan samun nasara ba. Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na da yakinin cewa, sake bullowar hare-haren kungiyar Boko Haram na da nasaba da sassauta karfin yakarsu daga jami'an tsaro saboda nasarorin da suka cimma a baya. Muddun ana son kai wa ga ci, dole ne a kullum a kasance cikin shirin tunkarar abun da ka je ya zo.

Gwamnati da jami'an tsaro kadai ba za su iya cimma nasara a yakar ta'addanci ba, domin hannu daya baya daukar jinka. Al'umma na da muhimmiyar rawar takawa a wannan aiki. Yadda suke ganin hakkin gwamnati ne ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu, su ma suna da hakkin kiyaye dokokin da ta gindaya da kuma ba jami'an tsaro hadin kai wajen gudanar da bincike da bada bayanan maharan don tabbatar da murkushe su baki daya. Idan har ba a samu cikakken hadin kan al'umma ba, to kwan gaba kwan baya kadai za a yi ta yi kan wannan batu, lamarin da ka iya ba wasu tsagerun damar bullo da na su salon fitina da rikici tare da hana al'umma kwanciyar hankali.

Kamar yadda waddancan gwamnoni suka ajiye banbancin siyasa da ra'ayi a gefe suka sanya buri guda na yaki da ta'addanci a gaba, ya kamata hukumomin tsaro daban daban da al'umma da gwamnatin su hada kai don ganin bayan wannan matsala ta bai daya, don samun kwanciyar hankalin kowa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China