Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Barkewar Annobar COVID-19 Ba Ta Canja Yanayin Bunkasuwar Kasashe Masu Tasowa Ba
2020-08-09 17:45:23        cri

Kasashen duniya sun dauki matakai iri daban daban domin fuskantar yaduwar cutar COVID-19, inda suka cimma sakamako iri daban daban bisa matakan da suka dauka da kuma halayen da kasashensu suke ciki. Kafin barkewar cutar COVID-19, kwararru a fannin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa sun taba yin hasashe cewa, babban taken karni na 21 shi ne bunkasuwar kasashe masu tasowa. Ya zuwa yanzu, duk da kasancewar matsalar yaduwar cutar COVID-19 a kasa da kasa, wadda ta kuma kawo sauye-sauyen dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, amma yanayin neman bunkasuwar bai daya a kasashe masu tasowa bai taba canjawa ba, bisa yadda kasashen suka fuskantar da yaduwar wannan annoba.

Da farko, dukkanin kasashe masu tasowa sun dauki matakan magance yaduwar cutar COVID-19 yadda ya kamata, inda suka yi nazari kan fasahohin yaki da cutar COVID-19, domin daukar matakan da suka dace wajen magance yaduwar cutar a kasashensu. Shi ya sa, cikin rubu'i na biyu, adadin raguwar karfin karuwar tattalin arziki a kasashe maso tasowa bai kai adadin na kasashe masu karfin ci gaba ba, wanda a kasar Amurka adadin ya kai 32.9%, yayin da 11.9% a kungiyar tarayyar Turai.

Haka kuma, kasashe masu tasowa sun fi son yin hadin gwiwa domin kare tsarin hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da kuma karfafa dunkulewar bil Adama. A wannan karo, galibin kasashe masu tasowa sun hada kansu da nuna goyon baya ga juna domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19. A farkon barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, kasashe masu tasowa da dama sun nuna goyon bayansu ga kasar Sin. Sa'an nan kuma, Sin ta samar musu taimako har sau sama da dari daya, bayan ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar a kasarta.

Hakan ya nuna cewa, kasashe masu tasowa suna dukufa wajen kiyaye tsarin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, inda ya nuna fatansu na karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama, domin neman ci gaba tare, wanda ya kasance hanyar neman ci gaba da ta dace da halin da kasa da kasa suke ciki. Shi ya sa, ana iya cewa, babban taken karni na 21 shi ne bunkasuwar kasashe masu tasowa na bai daya. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China