Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hana amfanin manhajar kasar Sin ya sabawa ka'idar tattalin arzikin kasuwa
2020-08-08 16:00:59        cri

A kwanakin baya ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa, gwamnatin Trump za ta dauki mataki kan wasu kamfanonin manhaja na kasar Sin wadanda a cewarsa suna kawo barazana ga tsaron kasar ta Amurka, inda ya ambaci TikTok, manhajar kasar Sin da ake amfani a ketare da WeChat, har ma shugaban kasar ya kara yin kashedin cewa, dole ne a sayar da manhajar TikTok ga kamfanonin kasar ta Amurka kafin ranar 15 ga watan Satumban dake tafe, yanzu haka ya gabatar da dokar shugaban kasa, inda Amurka ta haramta yin duk wata hulda da kamfanin fasahar kasar Sin na ByteDance, wanda ya mallaki shahararriyar manhajar nan ta TikTok, kuma dokar za ta fara aiki nan da kwanaki 45.

Amma tsohon babban mai ba da shawara kan dokoki na ma'aikatar shari'a ta Amurka Gene Kimmelman ya yi nuni da cewa, kalaman shugaban Amurka ba su da tushen doka a Amurka, kana wasu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, matakin da Amurka ta dauka matsin lambar siyasa ne da wasu 'yan siyasar kasar da wasu shugabannin manyan kamfanonin yanar gizon kasar suka yi cikin hadin gwiwa, lamarin da ya nuna adawar da 'yan siyasar Amurka suke nunawa ga kasar Sin, kuma hakan na nuna cewa, babu adalcin yin takara a kasar ta Amurka.

An lura cewa, ainihin dalilin da ya sa Amurka ta dauki matakin shi ne domin wannan manhajar ta TikTok ta kasar Sin ta fi kamfanonin Amurka samun karbuwa a wajen masu amfani da yanar gizo na kasashen yamma, yanzu haka ta dauki mataki kan manhajar ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa, hakika wannan rashin kunya ne.

Kan wannan batu, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani da kakkausar murya, inda ta bayyana cewa, Amurka tana siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya, haka kuma tana aiwatar da manufofin kyamar baki ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa, ba ma kawai matakin da Amurka ta dauka na hana yaduwar fasahar kasar Sin a fadin duniya ya sabawa ka'idar tattalin arzikin kasuwa ba, har ma ya sabawa ka'idar adalci ba tare da rufa rufa ba ta hukumar cinikayya ta duniya, ko shakka babu matakin ba zai yi mata kyau ba.(Marubuciya: Jamila daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China