Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko ya dace 'yan siyasar Amurka su ambaci "yanar gizo mai tsabta"?
2020-08-07 19:39:06        cri

A ranar 5 ga wata, agogon Amurka, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya sanar da wani shiri mai taken "yanar gizo mai tsabta" bisa fakewa da batun tsaron kasa, domin kawar da tasirin kamfanonin kasar Sin a bangarori biyar da suka kunshi sashen gudanar da harkokin yanar gizo, da runbun adana manhaja, da manhaja, da hidimar yanar gizo da masarrafar yanar gizo, a jiya Alhamis kuma, shugaban kasar ya sa hannu kan dokar shugaban kasa, inda Amurka ta kayyade harkokin kamfanonin dandalin sada zumunta na kasar Sin, makasudin matakin da Amurka ta dauka shi ne domin cire kasar Sin daga duniyar bayanai ta yanar gizo, ko shakka babu matakin nasa ya gamu da suka daga wajen al'ummun kasa da kasa daga duk fannoni.

Amma shirin da Pompeo ya gabatar bai dace ba, matsin lambar siyasa ne kan kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar Sin, shaidu sun nuna cewa, fasahohi da kayayyaki na kamfanonin kasar Sin suna da tsaro matuka.

Sabin haka, Amurka ita kanta tana kawo barazana ga tsaron sauran kasashen duniya ta hanyar satar bayanai ta yanar gizo, a don haka ake nuna shakku cewa, ko 'yan siyasar Amurka suna da ikon ambaton "yanar gizo mai tsabta"?

Yanzu haka daukacin kasashen duniya suna kara habaka cudanya da juna, yunkurin hana yaduwar fasahohin kasar Sin da 'yan siyasar Amurka ke yi ba zai yi nasara ba, saboda aikin sadarwar kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri, kana babbar kasuwar kasar Sin tana samarwa aikin sadarwa na sauran kasashen duniya damar samun ci gaba.

Sheihun malamin jami'ar California State University-Sacramento James Rae ya yi nuni da cewa, shirin Pompeo ya sabawa ka'idar hukumar cinikayya ta duniya, 'yan siyasa da 'yan kasuwa na sauran kasashen duniya su ma sun fahimci cewa, idan an amince da shirin, hakika zai lalata moriyar raya kamfanonin kasashensu.

A halin yanzu kasashen duniya suna kokarin raya kansu ba tare da rufa rufa ba, amma Pompeo wanda shi ne sakataren harkokin waje mafi muni a tarihin Amurka yana kawo illa ga ci gaban duniya, abun farin ciki shi ne an riga an gano cewa, shirin "yanar gizo mai tsabta" da ya gabatar wani abun dariya ne.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China