Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping na fatan Bankin AIIB zai taka muhimmiyar rawar raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam
2020-08-05 16:03:17        cri

A kwanakin baya ne, aka gudanar da taron shekara-shekara karo na 5 na bankin zuba jarin samar da ababen more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice ta kafar bidiyo. An kaddamar da ayyukan bankin na AIIB ne a shekarar 2016, bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar kafa shi a shekarar 2013.

A lokacin kafuwarsa, bankin na da mambobi 57, amma yanzu haka, bankin na da mambobi da suka kai 102, daga nahiyoyi 6 ciki hadda kasashen Asiya, da Turai, da Afirka, da Arewacin Amurka, da kudancin Amurka da kuma Oceania.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaba Xi, ya ce yayin da duniya ke kokarin dakile yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, dan Adam yana da makoma ta bai daya. Ko shakka babu, ta hanyar nuna goyon baya da hada kai tare ne kawai za a iya warware matsalolin da ake fuskanta, da kara yin hakuri da juna wajen tafiyar da harkokin duniya, da kare tsarin cudanyar bangarori da dama. Kamata ya yi bankin AIIB ya kasance wani sabon dandali tsakanin kasashe mambobinsa, wanda zai inganta samun bunkasuwa tare, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam.

Masana daga sassa daban-daban na duniya, sun yaba matuka da shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, suna masu imanin cewa, bankin zai bunkasa ci gaba na bai daya, baya ga zama wani sabon dandalin raya alakar bangarori daban-daban. A cewarsu, hukumomi kamar bankin AIIB na da muhimmanci, musamman ga kasashe masu tasowa, ta yadda za su ci gajiyar bankin wajen kara bunkasa ababan more rayuwarsu, da masana'antu da bangaren aikin gona har ma su samu ci gaba kamar sauran kasashen duniya.

A hannu guda kuma, shigar kasashen na Afirka a dama da su a harkokin bankin, zai ba su damar rage gibin ci gaban dake tsakaninsu da sauran kasashe, sabanin yadda hukumomin kudi irinsu bankin duniya, da IMF ke gindaya tsaurarran sharuddan rance ko ma tallafi ga kasashen kafin su amfana da ko wadanne irin tsare-tsare da suka bullo da su.

A don haka, kafa bankin AIIB wata muhimmiyar dama ce ta musamman ga kasashe masu tasowa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China