Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin tsakiya na kasar Sin ya sha alwashin ci gaba da kara bude kofa a fannin hada hadar kudade
2020-08-04 10:45:45        cri

Babban bankin tsakiya na kasar Sin ko PBOC a takaice, ya sha alwashin ci gaba da kara bude kofa a fannin hada hadar kudade, ta hanyoyi masu inganci kuma bisa tsari.

Mahukuntan bankin sun bayyyana hakan ne, yayin zaman gabatar da rahoton aikin sa na bana, wanda ya gudana ta kafar bidiyo. A cewar su, bankin na da nufin aiwatar da cikakkun kudurorin bunkasa zuba jarin waje na kasar Sin, da kyautata yanayin zuba jarin waje, da kara rage sassan da masu jarin waje ba su da izinin shiga.

Sauran fannonin sun hada da kara shigar da kudin kasar RMB cikin kasuwannin duniya, da fadada gogayyar sa da sauran kudaden kasa da kasa cikin kyakkyawan yanayi, tare da hade ka'idojin lura da musayar kudaden waje da ake amfani da su, a hada hadar takardun lamuni na kasar Sin.

Kaza lika babban bankin na Sin, ya ce zai zurfafa shiga harkokin jagoranci a fannin hada hadar kasuwanci ta duniya, da ba da kariya ga manufar cudanyar sassa daban daban. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China