![]() |
|
2020-08-02 18:39:03 cri |
Game da zargin, a kwanan baya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, "sau da dama, mun riga mun nuna cewa, yanzu kasar Sin tana sahun gaba wajen nazarin allurar rigakafin cutar a duk fadin duniya, babu wajibi, kuma babu bukata da ta saci sakamakon sauran mutane. Amma yanzu muna damuwa, ko wata kasa wadda ta fi son satar bayanan sauran kasashen duniya, za ta saci fasahar da kasar Sin ta samu."
Maganganun Wang Wenbin gaskiya ne. Wasu tawagogin kasar Sin wadanda suke nazarin allurar sun ba da rahoto cewa, sun samu nasarar gwajin allurarsu a mataki na farko da na biyu. Yanzu ana gwajinsu a mataki na uku a wasu asibitocin kasar Sin da na sauran kasashen duniya, kamar na kasar Brazil wadanda suka nemi yin irin wannan hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin. Idan kasar Sin ta samu nasarar samun irin wannan allurar rigakafin cutar COVID-19, tabbas ne zata samar wa sauran kasashen duniya, kamar kasashen Afirka nan da nan.
Kasar Amurka ta ce, idan an ci nasarar samun allurar rigakafin cutar, dole ne ita ta riga sauran kasashen duniya yin amfani da allurar. Har ma ta kebe dalar Amurka biliyan 2 tana son sayen dukkan allurar daga hannun wasu kamfanonin Turai masu ruwa da tsaki idan sun yi nasarar samun allurar. Amma kasar Sin na bin manufar kafa wani tsarin zaman al'ummar bil Adama dake da kyakkyawar makomar bai daya a duk duniya, tana kuma kokarin yin hadin gwiwar sauran kasashen duniya wajen dakile annobar. A ranar 17 ga watan Yunin, lokacin da yake shugabantar taron kolin kasar Sin da kasashen Afirka ta kafar bidiyo domin dakile annobar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, bangaren Sin na darajta zumuncin da ya dade yana kasancewa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Har ma ya alkawarta cewa, idan kasar Sin ta yi nasarar samun allurar rigakafin cutar COVID-19, tabbas ne kasashen Afirka zasu riga sauran sassan duniya cin gajiyar allurar.
Cutar numfashi ta COVID-19 barazana ce ga bil Adama a duk duniya. A lokacin da muke kokarin shawo kanta, ya kamata mu girmama ilmin kimiyya maimakon siyasantar da shi. Yanzu kasar Sin ta kusan cin nasarar shawo kanta a cikin gida, amma abokanmu na Afirka har yanzu na cikin hali mai tsanani wajen fama da ita. Bari mu Sinawa da Afirkawa mu yi hadin gwiwa wajen tinkarar ta. Muna cike da imanin cewa, tabbas ne masu nazarin allurar rigakafin cutar za su ci nasarar samun allurar, kuma za a iya yin amfani da ita kan masu harbuwa da cutar. 'Yan Afirka wadanda suka harbu da cutar za su samu allurar an jima ba da dadewa ba. (Sanusi Chen)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China