![]() |
|
2020-08-01 16:12:58 cri |
Irin wannan kudurin da aka sanar, wani mataki ne na musamman da gwamnatin yankin Hong Kong ta dauka, domin sanya zaman lafiyar jama'a gaba da komai a lokacin da ake fama da cutar COVID-19, al'amarin da ba kare lafiya da tsaron al'umma kadai zai yi ba, har ma da tabbatar da sahihancin zaben 'yan majalisar dokokin yankin cikin adalci, wanda ya dace da ka'idojin kasa da kasa.
Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa, zuwa tsakiyar watan Yulin bana, akwai kasashe ko yankuna akalla 70 wadanda suka jinkirta gudanar da zabe sakamakon yaduwar cutar COVID-19. Da ma zabe wata hanya ce da ake bi wajen shimfida demokuradiyya, kuma babbar ma'anarta ita ce, sanya moriya da zaman lafiyar al'umma a gaban komai.
Game da batun rashin guraban majalisar dokokin Hong Kong sanadin dage zaben, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin zai yanke shawara ba tare da bata lokaci ba. Kuma ana da yakinin cewa, gwamnatin Hong Kong za ta iya gudanar da zaben a yayin da take kokarin dakile annobar, domin tabbatar da zaman karko da dauwamammen ci gaba a wurin.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China