2020-07-31 13:53:31 cri |
Gobe 1 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru 93 da kafuwar rundunar 'yantar da al'ummar Sinawa, wato PLA a takaice. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku wasu sojojin kasar Sin wadanda suke sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan a madadin MDD.
A watan Yulin shekarar 2007, yayin taron kwamitin sulhu na MDD, aka zartas da kudurin jibge wata rundunar sojin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, wadda take kunshe da sojoji dubu 25 wadanda suka fito daga kasashe daban daban, ciki har da kasar Sin. Sabo da haka, a watan Oktoban shekarar 2007, kasar Sin ta fara tura tawagogin sojojin injiniya zuwa yankin Darfur har sau 15 kawo yanzu. Du Jingbo, hafsan dake jagorantar rundunar sojin injiniya ta kasar Sin dake tabbatar da zaman lafiya a kasar Sudan yanzu ya bayyana cewa, "Rundunarmu wadda take kunshe da sojojin injiniya wajen 200 ta isa yankin Darfur a ran 18 ga watan Disamban shekarar 2018, wato mun riga mun yi kusan watanni 20 muna sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya a yankin. Muhimman ayyukan da aka ba mu su ne, gyara hanyoyin mota da wasu filaye, kamar filin saukar jiragen sama da wasu gine-gine dake cikin yankin da hukumomin MDD dake yankin Darfur suke. Bayan isowarmu yankin, a kullum muna kokarin sauke nauyin dake wuyanmu domin tabbatar da zaman lafiyar yankin, da kuma kare mutuncin sojojin kasar Sin."
A lokacin da sojojin injiniya na kasar Sin suke sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur na Sudan, sun kuma bayar da gudummawarsu wajen taimakawa takwarorinsu na sauran kasashe wadanda su ma suke tabbatar da zaman lafiya a Sudan, da al'ummar wurin. A watan Agustar bara, wato a lokacin damina, cikin gaggawa, suka gyara wata muhimmiyar hanyar mota, wato hanyar mota daya tilo dake hade garin Gelo da sauran sassan kasar, domin tabbatar da sufurin kayayyakin jin kai na MDD da na manoman wurin. Sakamakon haka, manoman wurin sun yaba da aikin da sojojin kasar Sin suka yi cewar, "sojojin kasar Sin sun zo sun taimaka mana cikin sahihanci."
Aikin tabbatar da zaman lafiya aiki ne dake cike da wahalhalu da hadura sosai. Du Jingbo ya bayyana wani al'amari mai hadari da sojojin kasar Sin suka gamu da shi a yankin Darfur.
"Wani al'mari mafi hadari da muka gamu shi, shi ne, an ba mu umarnin gyara wata hanyar dake cikin yankin dutse. Nisan dake tsakanin inda muke aiki da tashar bincike ta 'yan tawaye na wurin bai kai mita 300 ba. Mun ga manyan bindigoginsu da idanunmu, a hakika dai, sojojinmu sun shiga dan damuwa."
Sanin kowa ne, yankin Darfur na Sudan yana cikin babban hamadan Sahara, a kan samu mummunan yanayi. Wata hukumar MDD ce take kula da aikin samar da kayayyakin abinci ga sojojin tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa dake yankin. A kan samar musu kayayyakin abinci ne kowane rabin wata, amma idan an samu mummunan yanayi, ko hanyar mota ta katse, mai yiyuwa a samar musu kayayyakin abinci sau daya a wata daya.
Annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ta barke a bana, ta kawo sabon kalubale ga rundunonin sojojin tattabatar da zaman lafiya a yankin. Du Jingbo ya bayyana cewa, "Bayan barkewar annobar a yankuna, inda muke sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya, a lokacin da muke aiki, dole ne mu nemi dabarun rage mu'amalarmu da mutanen wurin. Sabo da haka, yanzu a lokacin da muke kokarin sauke nauyin dake wuyanmu, muna kuma yin aikin rigakafi da dakile annobar."
Sabo da rundunonin sojin kasar Sin sun bayar da gudummawa sosai wajen tabbatar zaman lafiya a yankin Darfur na Sudan, sun samu yabo sau da dama daga wajen hukumar musamman da MDD da AU suka kafa a yankin. Laftana janar Carlos Humberto Loitey, mai ba da shawara kan harkokin soja na MDD ya yaba yana mai cewa, rundunonin sojin injiniya na kasar Sin sun bayar da muhimmiyar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma sake gina yankin Darfur. (Sanusi Chen)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China