Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu COVID-19 a Afrika ya zarce 828,214
2020-07-27 09:19:09        cri

Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce yawan mutanen da aka tabbar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya kai 828,214 a ranar Lahadi.

Afrika CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika AU, ta ce yawan mace macen da aka samu masu nasaba da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 17,509 ya zuwa ranar Lahadi.

Cibiyar dakile cututtukan masu yaduwa ta kara da cewa, a halin yanzu, majinyata 484,038 ne suka warke a fadin nahiyar bayan sun sha fama da cutar ta COVID-19.

Kasar Afrika ta kudu, inda aka samu rahoton adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar kimanin 434,200, ita ce kasar da annobar ta fi yiwa illa a Afrika, sai kuma kasashen Masar, Najeriya, Algeria da Morocco dake bi mata baya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China