![]() |
|
2020-07-26 15:54:11 cri |
Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiyar ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bayyana cikin sabbin alkaluman da ta fitar cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun harbu da COVID-19 ya karu a fadin nahiyar daga 787,501 a ranar Juma'a zuwa 810,008, ya zuwa tsakar ranar Asabar.
Rahoton na Africa CDC ya kara da cewa, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar ya karu zuwa 17,088 a ranar Asabar, daga adadin mutane 16,697 a ranar Juma'a.
Hukumar dakile yaduwar cutukan ta nahiyar tace, jimillar majinyata 462,374 ne suka warke bayan sun sha fama da cutar ta COVID-19 a Afrika ya zuwa yanzu.
Kasar Afrika ta kudu ce cutar tafi yiwa illa, sai kasashen Masar, Najeriya, Algeria da Morocco, dake bi mata baya.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China