Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasuwanci ta Intanet yana taimakawa ga ci gaban zamantakewar al'umma
2020-07-25 15:38:09        cri

Jama'a ko kun san cewa, a halin yanzu zaman rayuwar mutanen kasar Sin yana dogara kwarai kan wayar salula da kuma yanar gizo ta Intanet? Alal misali, idan an tashi da safe, a kan yi amfani da wayar salula domin odar abincin karya kumallo. Idan ana son zuwa wani wuri, a kan yi amfani da wata manhaja a wayar domin hawan keken haya. Idan ana son sayen wani abu, a kan saye shi ta kafar Intanet maimakon a je shago. A lokacin da ake fama da yaduwar cutar COVID-19, ba dole a taru a ofis ba, wato duk inda suke, ma'aikata za su yi amfani da wata manhaja iri daya a wayarsu domin samun damar gudanar da ayyuka tare. Salon tattalin arziki ko kuma kasuwancin da ake yi ta kafar Intanet yana kawo sauye-sauye ga zaman rayuwar mutanen kasar Sin, al'amarin da zai amfana wajen raya zaman al'umma mai matsakaicin wadata a kasar.

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron karawa juna sani tare da shugabannin wasu manyan kamfanonin kasar a kwanan nan, ya jaddada cewa, ya zama dole a yi kirkire-kirkire ga harkokin kimiyya da fasaha, da gaggauta nazartar sabbin fasahohi masu muhimmancin gaske, domin lalibo sabuwar hanyar neman ci gaba. Bisa takardar bayani kan bunkasuwar cinikayya ta kafar Intanet na shekara ta 2020 da cibiyar nazarin harkokin sadarwa ta kasar Sin ta bayar, a shekara ta 2019, yawan karuwar cinikayyar da aka yi ta kafar Intanet ya kai Yuan tiriliyan 35.8, kwatankwacin dala tiriliyan 5.1.

Kasuwanci ta kafar Intanet yana kara biyan bukatun al'umma na yau da kullum. Alal misali, idan ana amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato fasahar zamani ta AI, za'a iya fassara maganar wani mutum cikin yaruka sama da 10 a lokaci guda, abun da zai iya biyan bukatun al'umma na fadada hanyoyin mu'amala da baki 'yan kasashen waje. Babu shakka, ingantuwar fasahar sadarwar zamani ya zama sabon karfi wajen kyautata zaman rayuwar al'ummar kasar Sin.

A dayan bangaren ma, fasahar sadarwar zamani, musamman fasahar gudanar da cinikayya ta kafar Intanet yana gaggauta canja salon sana'o'in gargajiya, musamman a fannin kere-kere, da jigilar kayayyaki da sauran wasu sana'o'in bada hidima. Kamar yayin da ake kokarin kandagarkin yaduwar cutar COVID-19, an kara bullo da dabarun gudanar da ayyuka da karatu ta kafar sadarwar Intanet, al'amarin da ya kirkiro sabbin hanyoyin habaka tattalin arzikin kasar Sin.

Salon tattalin arziki da kasuwanci ta kafar sadarwar Intanet za su ci gaba da bunkasa a duk fadin duniya baki daya. A matsayin babbar kasa a fannin kere-kere da yawan mutanen dake amfani da Intanet, ya kamata Sin ta ci gaba da gudanar da bincike kan fasahohin sadarwar zamani, da canja tsohon salon tattalin arziki, ta yadda karin jama'a za su iya cin gajiyar bunkasuwar fasahar, da biyan bukatunsu na zaman rayuwar yau da kullum. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China