Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya bukaci a inganta kungiyoyin hada kan manoma bisa yanayin da ake ciki a sassan kasar
2020-07-23 13:42:23        cri


Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin tsakiyar jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, ya karfafa gwiwar raya kungiyoyin hada kan manoma bisa yanayin da ake ciki a sassa daban daban na fadin kasar.

Shugaba Xi ya bayyana hakan da yammacin ranar Laraba, a lokacin rangadin ziyarar duba aikin wata kungiyar hadin kan manoma a yankin Lishu, na birnin Siping dake lardin Jilin na kasar.

Bayan nazari kan alfanun da kungiyoyin hada kan manoma ke haifarwa ga mambobinta, Xi ya yabawa muhimmin kokarin da mambobin suka gudanar wajen lalibo hanyoyin raya cigaba da suka dace da su, da daga matsayin aikin gona na zamani, tare da yin amfani da ingantattun fasahohin aikin gona, domin samar da babbar moriya ga al'umma a fannonin aikin gona.

Shugaba Xi, ya karawa manoma kaimi dasu cigaba da bunkasa kwarewar da suke da ita, kana ya bukace su da su kara himma domin bullo da wasu hanyoyi na musamman da zasu kara bunkasa kungiyoyin hada kai a duk fadin kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China