Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa dandalin CMG dake amfani da fasahohin 5G da 4K ko 8K don gabatar da shirye-shirye
2020-07-23 10:42:52        cri

Jiya Laraba an yi bikin kafa dandalin babban gidan rediyo da telibiji na kasar Sin na CMG dake amfani da fasahohin zamani na 5G da 4K ko 8K, don gabatar da shirye-shirye a nan birnin Beijing.

Mamban taron tsara tsarin shirya-shiryen CMG Jiang Wenbo ya nuna cewa, CMG ta gaggauta gina wannan dandali mai amfani da fasahar zamani, bisa ruhin shugaba Xi Jinping na kara karfin kirkire-kirkire, kuma an yi amfani da wannan shiri don zamanintar da fasahar CMG, don ta ba da jagoranci ga sha'anin yada labarai, da yin amfani da fasahar zamani cikin sauri.

Wadannan dandali sun kunshi ayyuka masu dimbin yawa, ciki hadda kafa tsarin gabatar da shirye-shirye ta hanyar yin amfani da fasahar 5G da 4K ko 8K a birnin Beiing hedkwatarsa, da kuma tashar yada labarai ta Shanghai, da gina manyan na'urori, ciki hadda tsarin Intanet mai daukar shirye-shirye na HD da dai sauran fasahohi.

Yawan kudin da aka zuba ga wannan shiri ya kai kudin Sin RMB yuan miliyan 420, ana kuma sa ran kammala wannan aiki cikin shekaru biyu masu zuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China