Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Boko Haram ta kashe ma'aikatan agaji 5 a Najeriya
2020-07-23 09:51:56        cri
Wani faifan bidiyo da kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta fitar a ranar Laraba ya nuna yadda aka kashe ma'aikatan ayyukan jin kai wadanda aka yi garkuwa dasu kwanan nan a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Ma'aikatan, wadanda ke wakiltar hukumomi da suka hada da hukumar bada agajin gaggawa ta jaha, da kungiyoyin agaji na Action Against Hunger, da Rich International, da kuma International Rescue Committee, dukkan ma'aikatan an kashe su, kamar yadda bidiyon ya nuna.

Kungiyar 'yan ta'addan ta nemi a biyata kudin fansa na kusan dala dubu 500 kafin su sako ma'aikatan.

A ranar Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kashe ma'aikatan, inda ya bada tabbacin gwamnati zata cigaba da yin bakin kokarinta domin tabbatar da ganin an kakkabe duk wani burbushin Boko Haram.

Mayakan kungiyar Boko Haram, masu da'awar kafa daular musulunci a arewacin Najeriya, sun sha kaddamar da hare hare kan fararen hula da sojoji a jahohin Adamawa, Borno, da Yobe, duk da kokarin da hukumomin tsaron Najeriyar ke yi.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China