Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a bar kasuwa ta yi halinta
2020-07-22 14:27:45        cri



Babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana, shugaban kasar, wanda har ila shi ne shugaban kwamitin kolin sojojin kasar, Xi Jinping, ya jagoranci wani taron karawa juna sani tare da 'yan kasuwa a jiya Talata, inda ya jaddada cewa, bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta kafa, gami da kara kyautata tsarin tattalin arziki mai baiwa kasuwa damar yin halinta karkashin salon gurguzu, abun da ya sa kasuwannin kasar suka dada bunkasa. Amma annobar mashako ta COVID-19 tana haifar da babbar illa ga tattalin arzikin kasar Sin da na duk duniya baki daya, don haka akwai kasuwannin kasar da dama wadanda suke fuskantar babban kalubale wanda ba'a taba ganin irinsa ba a tarihi. Shi ya sa ya kamata a kara azama domin ganin kasuwa ta yi halinta, da ma bunkasa harkokin kasuwanci, ta yadda sha'anin kasuwanci zai taka muhimmiyar rawa tare da samun gagarumin ci gaba.

A wajen taron karawa juna sanin, akwai shugabannin wasu manyan kamfanoni 7, wadanda suka gabatar da jawabansu, inda suka bayar da shawarwari kan batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu, da kare kasuwanni, da kara yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da zurfafa garambawul ga kamfanoni daban-daban, da kuma karfafa gwiwar mutane masu basira da sauransu.

Bayan haka, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu wajen ganin bayan yaduwar cutar a kasar Sin, kuma tattalin arziki yana samun farfadowa, wanda ya wuce hasashen da aka yi. Ya ce ya kamata mu karfafa imani, da haye wahalhalu, domin rage hasarar da annobar ta haifar, domin samun ci gaban tattalin arzikin kasa yadda ya kamata.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasuwa ita ce jigon raya harkokin tattalin arziki a kasar Sin, wadda ke samar da isassun guraban ayyukan yi, da taimakawa ci gaban fasahohi. Tun bullar cutar COVID-19, 'yan kasuwa da kamfanoni daban-daban sun nuna himma da kwazo, wajen shiga ayyukan tinkarar annobar, wadanda suka samar da goyon-bayan kayayyaki masu tarin yawa ga ayyukan dakile annobar.

Shugaba Xi ya bayyana cewa:

"A daidai wannan lokaci, ina son mika babbar godiyata ga kamfanoni mallakin gwamnati, da kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanoni masu jarin waje, da kamfanonin jarin Hong Kong da Macau da Taiwan, tare kuma da 'yan kasuwa masu zaman kansu, saboda irin gudummawar da suka bayar ga ayyukan ganin bayan annobar, da raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma."

Xi ya kuma jaddada cewa, hukumomi daban-daban a kasar Sin sun bullo da wasu muhimman matakai na goyon-bayan 'yan kasuwa da kamfanoni daban-daban, wato a bar kasuwa ta yi halinta, ta yadda za ta samu karin ci gaba. Na farko, ya kamata a taimaki kamfanonin da suke cikin mawuyacin hali. Wato a kara aiwatar da manufar tattalin arziki yadda ya kamata, da ci gaba da rage harajin da ake bugawa, domin 'yan kasuwa da kamfanoni su amfani manufofin nuna gatanci kai-tsaye. Na biyu, ya kamata a nuna kwazo wajen samar da wani yanayin kasuwanci na kasa da kasa bisa doka da oda. Wato a ci gaba da aiwatar da dokar kare al'umma, da sauran ka'idojin da abun ya shafa, da kiyaye hakki gami da 'yancin kamfanoni daban-daban, ciki har da na gwamnati, da masu zaman kansu, da na jarin waje, da kara aiwatar da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, da ci gaba da saukaka musu matakan shiga kasuwanni, da gudanar da kasuwanci da zuba jari. Na uku shi ne, kamata ya yi a kyautata alaka tsakanin 'yan siyasa da 'yan kasuwa. Wato an bukaci jami'an gwamnati da 'yan kasuwa su yi mu'amala yadda ya kamata ba tare da wata rufa-rufa ba, da kara sanin me abun da 'yan kasuwa suke tunani, da abun dake damunsu, da kara sauraren shawarwarinsu a yayin da ake tsara manufofin kamfanoni.

Haka kuma, ya zama dole a yaki matsalar cin hanci da karbar rashawa, wadda za ta illata dangantakar dake tsakanin 'yan siyasa da 'yan kasuwa, da ma yanayin kasuwanci baki daya. Na hudu wato na karshe shi ne, ya kamata a kara maida hankali kan goyon-bayan bunkasuwar 'yan kasuwa masu zaman kansu, da taimaka musu wajen warware matsalolin da suke fuskanta, a fannonin da suka shafi kudin haya, da haraji, da kudin inshora da samun jari da makamanta.

Shugaba Xi Jinping ya nanata cewa, bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, an kara samun wasu gogaggun 'yan kasuwa, wadanda suka taimaka sosai ga ci gaban kamfanonin kasar Sin a duk fadin duniya. Xi ya kuma bukaci 'yan kasuwan su jagoranci kamfanoninsu, wajen haye wahalhalun da suke fuskanta, da ci gaba da kyautata halinsu a fannonin da suka jibanci kishin kasa, da yin kirkire-kirkire, da nuna sahihanci, da sauke nauyin dake wuyansu, ta yadda za su kasance tamkar muhimmin karfi wajen raya tattalin arziki da samun ci gaba mai inganci a kasar Sin. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China