Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ayarin mata masu duba sassan jirgin kasa a Manzhouli na Sin
2020-07-22 09:22:03        cri

Manzhouli dake jihar Mongolia ta gida mai cin gashinta na arewacin kasar Sin, ita ce tashar kan tudu mafi girma dake kan iyakar Sin da Rasha, kuma tasha mafi muhimmanci karkashin shawarar "Ziri daya da Hanya Daya". Wani ayarin mata masu duba sassan jirgi dake karkashin Madam Chen Jia, suke da alhakin duba jiragen kasan dakon kaya na Rasha, da kuma tabbatar da ingancin jiragen sufuri na kasashen waje. Ana kiran Chen da sauran mambobin ayarin 4, da "furanni 5 na tashar".

Tashar Manzhouli, dake sansanin sauke kayayyaki na Qiqihar ta kamfanin sufurin jiragen kasa na Harbin, ta kafa wani ayarin mata masu duba jirgi a watan Maris na 1986. Chen Jia ita ce shugaba ta biyu ta ayarin, kuma ta shafe shekaru sama da 10 tana aiki a tashar.

"Aikinmu shi ne duba jiragen kasa na dakon kaya na kasar Rasha da za su shigo kasar Sin. Muna duba ko akwai wani abu a jikin jirgin da ya bata ko ya lalace, kuma muna nazartar yanayin da jiragen ke ciki", cewar Chen.

Wasu na ganin wannan aikin ya fi dacewa da maza, domin yana da wahala. Amma Chen na ganin cewa, mata suna da kula sosai, don haka wannan na taimakawa aikin.

Bisa la'akari da cewa, layukan dogo a Rasha sun fi na Sin fadi, dole ne jiragen da suka fito daga Rasha su sake loda kayayyakinsu cikin jiragen kasar Sin a tashar Manzhouli, kafin a yi safararsu zuwa sauran yankunan kasar Sin.

Chen Jia da sauran mambobin ayarinta, su kan tunatar da kansu a koda yaushe cewa, aikin da suke yi na kunshe da kare martabar kasa. Yanayin lokutansu na aiki da cin abinci da hutu, ya bambanta da yadda aka saba. A duk lokacin da jiragen kasa da suka iso daga Rasha, nan take ayarin ke fadawa aiki.

Yawancin jiragen kasa masu dakon kaya na da sassa sama da 10,000. Yayin da suke aiki, dole ne su maimaita wasu abubuwa uku, wato dukawa kasa da kallon sama da kuma jingina. Yayin wa'adin aiki 1, sun kan duba tarago 300, wanda ke nufin su kan maimaita wadancan abubuwa har sau 8,000.

Lokacin hunturu kan shafe watanni 6 a Manzhouli, kuma yanayin da daddare a lokacin hunturu kan kai maki 40 kasa da sifili bisa ma'aunin Celsius. Matsanancin yanayin na tattare da kalubale ga aiki a waje. Amma shi ke inganta karfin kudurin Chen da mambobin ayarinta.

Chen ta furta cewa, "duk da cewa muna sa inifom mai kauri, muna jin sanyi. Galibi, a kan dauki mintuna 40 wajen duba sassan jirgi. Amma a kan dauki kimanin sa'o'i 2 idan aka yi ruwa ko dusar kankara. Duk rashin kyan yanayi, dole ne mu yi wa jiragen duban kwakwaf ".

A wata shekara, an yi dusar kankara sosai a jajibirin bikin bazara. Bisa la'akari da yadda kankara ya lullube galibin sassan jiragen, sai da Chen da sauran mambobinta suka rika cire kankara da hannayensu domin duba taragon. Sai da suka dudduba jirage 6 a wannan dare.

Ban da Madam Chen Jia, sauran matan biyar kwararru ne dake da gogewa. Zhang Cuiyan, ita ce mafi yawan shekaru a cikin ayarin, tana da gogewar aikin duba jirgi na tsawon shekaru 20. Ta ce, hadin kan mambobin shi ne kashin bayan shawo kan duk wata matsala. "muna nan kamar 'yan uwa", cewar Zhang.

Chen da abokan aikinta sun yi karatu sosai domin koyon harshen Rasha, saboda dole ne su yi mu'amala da ma'aikata daga Rasha. Chen na da wani littafin dake cike da kalmomin aiki, a cikin harshen Sinanci da na Rashanci. Chen ta ce, sun kuma tsara wani jadawali na kalmomi masu kama game abubuwan da suka lalace, wannan na saukaka musu aiki.

Cikin shekaru 34 da suka gabata, ayarin matan ya gano sassan jirgi da suka lalace sama da sau miliyan 1.5. Idan da ba a gano sassan ba, lalacewarsu ka iya haifar da abun da zai lakume kimanin Yuan miliyan 700, kwatankwacin dala miliyan 101.

"Dole ne mu yi aikinmu yadda ya kamata, domin tabbatar da jiragen na aiki da kyau. Lalacewar wasu sassan ba wata matsala ba ce sosai, amma za su iya haifar da hatsari mai tsanani idan ba a gano da wuri ba", cewar Chen.

Ita da sauran mambobinta sun samu yabo daga ma'aikatan Rasha saboda kwarewarsu. Wani ma'aikacin hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Rasha, mai suna Pavel, ya kai shekaru 10 yana aiki a Manzhouli. Ya kulla abota mai karfi da ayarin.

Chen ta yi tsokacin cewa, "bayan shafe shekaru da dama ana aiki tare, mun fahimci juna sosai. Mu kan tattauna da juna, kuma mu kan lalubo mafita idan mun gamu da matsala. Duba jirgi na bukatar sanin nauyin dake wuyanka, da kuma kwazo, amma kuma akwai dadi. Na kan yi farin ciki a duk lokacin da na yi nasarar kammala duba jirgi. Na kan jinjinawa aikina ".

A yanzu, Chen da abokan aikinta na duba jirage 20 a ko wacce rana. Jimilar tazarar da su kan yi tattaki yayin wa'adin aiki guda a rana, ta zarce kilomita 20.

Ayarin matan sun karbi lambobin yabo da dama daga matakin lardi da kasa saboda jajircewarsu. A ranar 6 ga watan Maris na 2019, a madadin abokan aikinta, Chen Jia ta karbi lambar yabo daga kungiyar mata ta kasar Sin a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing.

"Na yi matukar farin ciki da samun lambar yabon a babban dakin taron jama'a. zai karfafa mana gwiwar ci gaba da bada gudunmuwar karfi da basirarmu ga aikinmu," cewar Chen.

A ranar 3 ga watan Mayun 2019, sashen wayar da kan jama'a na kwamitin tsakiya na JKS da kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Sin, suka gabatar da labaran Ma'aikata Mafi Kyau na 2019, wato ma'aikata mafi hazaka. Chen na cikin mutane 9 da suka karbi lambar karramawar.

Da aka tambaye su dalilin nacewa ga aikinsu, Chen ta bada amsa a madadin abokan aikinta. "Mun zauna a nan ne saboda muna da hazaka kamar takwarorinmu maza, kuma muna da karfin imanin hidimtawa kasarmu".(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China