Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO:Abin damuwa ne yadda annobar Covid-19 ke saurin yaduwa a Afirka
2020-07-21 14:53:25        cri





Babban darektan hukumar lafiya ta duniya(WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya 20 ga wata cewa, har yanzu nahiyar Amurka ta kasance shiyyar da annobar Covid-19 ta fi kamari a fadin duniya. Sai kuma Michael Ryan, jami'i mai kula da shirye-shiryen gaggawa na hukumar ya ce, abin damuwa ne yadda annobar ke kara saurin yaduwa a kasashen Afirka, kuma ya kamata kasashen su dauki darasi daga halin da kasar Afirka ta kudu ke ciki.

Kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta samar ta nuna cewa, kawo jiya 20 ga wata, yawan al'ummar da suka harbu da cutar Covid-19 ya kai sama da miliyan 14 a fadin duniya, a yayin da wasu sama da dubu 600 suka gamu da ajalinsu. A gun taron mamema labarai da aka shirya a jiya, babban darektan hukumar, Mr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, har yanzu, nahiyar Amurka ta kasance shiyyar da annobar ta fi kamari a fadin duniya. Alkaluman da hukumar lafiyar ta samar sun shaida cewa, gaba daya yawan mutanen da suka kamu da cutar ya zarce miliyan 7.5 a nahiyar ta Amurka, a yayin da wasu sama da dubu 300 daga cikinsu suka mutu, adadin da ya kai sama da rabi na wadanda suka halaka sakamakon cutar a duniya baki daya. A cewar babban darektan, duk da cewa mutane daga sana'o'i daban daban dukkansu sun sha illolin da annobar ke haifarwa, amma masu karamin karfi ne suka fi kasancewa cikin hadari, musamman ma 'yan asali mazauna shiyyoyi daban daban sama da miliyan 500 a fadin duniya. Ya ce, "Duk da cewa annobar Covid-19 barazana ce ga 'yan asalin mazauna sassan duniya baki daya, hukumar WHO na matukar damuwa da tasirin da take haifarwa ga 'yan asalin nahiyar Amurka, a yayin da nahiyar ke ci gaba da kasancewa shiyyar da annobar ta fi kamari. Ya zuwa ranar 6 ga wata, akwai 'yan asali mazauna nahiyar sama da dubu 70 da aka ba da rahoton kamuwarsu da cutar, a yayin da sama da dubu 2 daga cikinsu suka mutu."

Baya ga halin da ake ciki a nahiyar Amurka, saurin yaduwar annobar a nahiyar Afirka ma ta jawo hankalin hukumar. Mr. Michael Ryan, jami'i mai kula da shirye-shiryen gaggawa na hukumar ya ce, annobar na gaggauta yaduwa a nahiyar, a cikin makon da ya gabata, masu harbuwa da cutar sun karu cikin sauri a kasashen Afirka da yawa, misali an samu karuwar da ta kai kaso 50% a kasar Madagascar, a yayin da adadin ya kai kaso 57% a Zambia, sai kuma kaso 51% a Zimbabwe. A kasar Afirka ta kudu kuma, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya zarce dubu 360, adadin da ya sanya kasar ta zama ta biyar daga cikin kasashen da suka fi yawan al'ummar da suka harbu da cutar. A game da hakan, Mr. Michael Ryan ya yi nuni da cewa, ya kamata sauran kasashen nahiyar su koyi darasi daga yanayin da kasar ke ciki. Ya ce, "A shiyyar da ke kudu da Sahara, cutar na kara saurin yaduwa a kasashe da dama. A ganina, ya kamata a dauki lamarin da muhimmanci. Sai dai abin bakin ciki shi ne, yanayin da ake ciki a Afirka ta kudu ka iya zama wata alama, wadda ke yi wa sauran sassan nahiyar gargadi dangane da abin da ka iya faruwa gare su."

 

Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban darektan hukumar WHO ya kuma sa kaimin kasa da kasa da su dauki dukkan matakan da suka wajaba na kadagarkin cutar. Ya ce, "ba lalle ba ne mu jira alluran rigakafin cutar, abin da ya kamata mu yi yanzu shi ne ceton rayukan al'umma." Ya jaddada muhimmancin bin bahasin wadanda suka taba cudanya da mutanen da suka harbu da cutar, da kuma horar da ma'aikatan lafiya da su bi gida gida domin gano masu cutar da kuma wadanda suka yi cudanya da su, sabo da hakan zai iya taimakawa ga katse yaduwar cutar. Aikin na da muhimmanci a kasashe komin yanayin da suke ciki, sabo da zai iya kare yaduwar cutar daga wani zuwa wasu, har ma zuwa unguwanni. A yayin da kasashe ke bude kofarsu sannu a hankali, daukar matakan gaggawa dangane da sabbin masu cutar da aka gano zai iya tabbatar da farfadowar tattalin arziki da kuma kare yaduwar cutar. Ya ce, "Idan ba mu san inda cutar take ba, lalle ba za mu kai ga shawo kanta ba. na sha nanata cewa, matakan da aka dauka na kulle wani birni zai iya taimakawa ga rage yaduwar cutar, amma ba zai iya hana yaduwarta kwata kwata ba. Don haka, bin bahasin wadanda suka taba cudanya da mutanen da suka harbu da cutar na da matukar muhimmanci."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China