![]() |
|
2020-07-19 16:07:52 cri |
Africa CDC, kwararriyar hukumar kiwon lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta sanar a ranar Asabar cewa a yanzu haka kasashen Afrika 40 suna karkashin cikakken tsarin rufe kan iyakokinsu, yayin da wasu kasashen 34 suka sabunta tsarin dokar kulle cikin dare a kasashensu a wani mataki na dakile bazuwar cutar ta COVID-19.
Ya zuwa ranar Asabar, adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 a fadin Afrika sun zarce 682,743, yayin da mutanen da cutar ta hallaka sun kai 14,671, kamar yadda alkaluman baya bayan nan na Africa CDC ya bayyana.
Hukumar dakile cutuka ta nahiyar ta ce, jimillar mutanen da suka warke bayan sun sha fama da cutar ta COVID-19 a Afrika ya kai mutane 362,071 ya zuwa yanzu. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China