Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don samar da ci gaba mai dorewa
2020-07-15 11:00:39        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a yayata kasancewar bangarori daban-daban da hadin gwiwar kasa da kasa, a wani mataki na samun ci gaba mai dorewa.

Zhang Jun wanda ya bayyana haka yayin zaman taron dandalin manyan jami'an siyasa na MDD kan ci gaba mai dorewa, ya ce, duniya na fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba cikin shekaru 100. Yana mai cewa, dunkulewar duniya ta taimaka matuka ga ci gaban tattalin arzikin duniya da yadda ake mallakar kayayyaki. Baya ga yadda ci gaban kimiyya da fasahar kere-kere yake hade bangarorin ilimi da ayyukan bil-Adama.

Jami'in na kasar Sin ya ce, yadda kasashen da tattalin arzikin ke bunkasa gami da kasashe masu tasowa ke tasowa, ya sauya tsarin siyasa da tattalin arzikin kasa da kasa. A halin da ake ciki, ra'ayi na kashin kai, da muzantawa, da ra'ayin ba da kariya, da adawa da dunkulewar duniya, suna dakushe ginshikin kasancewar bangarori daban-daban da dakula yanayin hadin gwiwar kasa da kasa. A gyefe guda kuma, cutar COVID-19 ke yin mummunan tasiri kan ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'a.

Ya ce, a yayin da duniya ke fama da yanayi mai sarkakiya, yana da muhimmanci matuka fiye da ko wane lokaci, a yi kokarin samun ci gaba da hanzarta aiwatar da ajandar dawwamammen ci gaba nan da shekarar 2030. Don haka, ya kamata dukkan bangarorin da abin ya shafa, su dauki managartan matakan yakar COVID-19, da kokarin farfadowa da raya tattalin arziki mai dorewa da zai shafi kowa, da kara kaimi da nuna tabbaci wajen hanzarta aiwatar da ajandar shekarar 2030.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China