Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya na fatan kawo karshen ayyukan 'yan bindiga a kasar
2020-07-14 10:03:18        cri
Babban hafsan tsaron Najeriya Gabriel Olonisakin ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, ayyukan 'yan bindiga a yankunan arewacin kasar zai zama tarihi.

Olonisakin ya bayyana haka ne, lokacin da ya ziyarci dakarun sabon shirin nan mai suna "Sahel Sanity" masu aikin kakkabe bata gari a yankin Faskari dake jihar Katsina. Shirin da ake fatan zai kakkabe batarin dake addabar ragowar jihohin Zamfara da Sokoto da Kaduna da jihar Niger.

Yana mai cewa, kaddamar da shirin wata alama ce dake nuna kudurin sojojin na magance dukkan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Ya ce, ko shakka babu, ayyukan bata garin zai zama tarihi, ta yadda jama'a za su koma gudanar da harkokinsu na rayuwa kamar yadda suka saba.

A baya-bayan nan dai, ayyukan 'yan bindiga, da satar mutane da sauran munanan ayyuka sun zama ruwan dare a wasu sassan arewacin Najeriya. Sai dai sojoji na cewa, suna samun galaba, ta hanyar hare-haren da suka kai musu. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China