Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Ghana ta ki amincewa da rufe makarantu yayin da ake fama da COVID-19
2020-07-14 09:54:05        cri
Gwamnatin Ghana ta ki amincewa da kiran da wani bangare na al'ummar kasar ya yi, da ta rufe manyan makarantun sakandare a fadin kasar, saboda yaduwar COVID-19 a makarantu.

Kawo yanzu, an samu masu cutar COVID-19 a manyan makarantun sakandare 14 daga cikin 16 dake larduna 6 na kasar dake yammacin Afrika. Baki daya, dalibai 35 cikin sama da 300,000 ne suka kamu da cutar.

Sai dai ministan yada labarai na kasar, Ursula Owusu Ekuful, ya shaidawa manema labarai cewa, za a fi kula da daliban a kebabben wuri, maimakon a bukaci su koma gida.

Ya ce , rufe makarantu ba shi ne hanya mafi dacewa ba, domin ba a san lokacin da cutar za ta kare ba. Yana mai cewa, a ganinsa, dalibai za su fi kasancewa cikin aminci a makaranta, wanda yake kebabben wuri, maimakon rufewa a tura su gida. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China