2020-07-11 17:34:53 cri |
Lin Lin ta bayyana a cikin jawabinta cewa, an kwace Hong Kong da karfin makamai daga hannun kasar Sin, inda ta kasance karkashin mulkin mallaka, kuma a shekarar 1997 aka maido da yankin karkashin mulkin kasar Sin, tana mai cewa, wannan abun farin ciki ne.
A cewarta, 2019, shekara ce ta bakin ciki a yankin Hong Kong, ganin cewa a wannan shekara yankin ya kasance wani wuri na tashin hankali. Ta ce kafofin watsa labaru da 'yan siyasar wasu kasashen ketare sun yi nufin halatta ayyukan nuna karfin tuwo da aka yi a yankin, kuma sun yi ta tsorata wadanda suke da bambancin ra'ayi da su.
Lin Lin ta kara bayyana cewa, jama'ar yankin Hong Kong ba za su yi hakuri da rikici ba. A watan Yunin bana, mazauna yankin miliyan 2.9 suka sanya hannu don nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin wajen tsara dokar kiyaye tsaron kasa a yankin. A cewarta, akwai bukatar su sake gina birninsu. Ba za su yarda a kara aikata rikici a Hong Kong ba, ta ce an riga an yi watsi da mulkin mallaka, don haka sai masu adawa da kasar Sin su nisanci yankin. (Bilkisu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China