Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta tabbatar da dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci yayin da yake tsaka da fuskantar bincike
2020-07-11 16:30:18        cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya amince da dakatar da Ibrahim Magu, mai rikon mukamin shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa (EFCC).

Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, ministan shari'a na kasar Abubakar Malami, ya ce an dakatar da shugaban na hukumar EFCC ne domin ba kwamitin shugaban kasar damar gudanar da bincike kansa ba tare da wani tarnaki ba, karkashin dokar gudanar da bincike da sauran dokoki masu nasaba.

Kwamitin shugaban kasar na bincike kan Magu, wanda jami'in dan Sanda ne, bisa zargin cin hanci da amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba da rashin biyayya da kuma ruf da ciki kan kudaden da aka kwato.

An dakatar da Ibrahim Magu ne a ranar Talata, kuma har zuwa yanzu 'yan sanda na tsare da shi yayin da kwamitin ke aiwatar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China