![]() |
|
2020-07-08 11:16:47 cri |
Bugu da kari, babu wanda ya kamu da cutar da ya shiga birnin Beijing daga kasashen ketare, kuma, babu mutum ko da daya da ake zaton mai iyuwa ya kamu da cutar ta COVID-19. Ba a samu kuma wanda ya kamu da cutar COVID-19 da bai nuna alamun kamuwa da cutar ba, wadanda suka shiga birnin Beijing daga kasashen ketare.
Hakan dai na nuna cewa, cikin kwanaki 2 da suka gabata, babu sabon wanda ya kamu da cutar a birnin Beijing.
Daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa ranar 7 ga watan Yuli, gaba daya, an tabbatar da mutane 335 dake dauke da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin, kuma mutane 307 daga cikinsu sun samu kulawa a asibitoci, yayin da mutane 28 suka warke. A halin yanzu kuma, ana sa ido kan masu dauke da cutar su 31, wadanda ba su nuna alamun kamuwa da ita ba. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China