Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lokaci ya yi da ya kamata Birtaniya ta fahimci cewa Hong Kong mallakin kasar Sin ne, ba nata ba
2020-07-07 14:58:06        cri

 

Har yanzu, batun dokar tsaron kasar Sin a kan yankinta na musamman na Hong Kong na ci gaba da daukar hankalin kasashen yammacin duniya da batun sam bai shafe su ba.

Ko a jiya Litinin, Jakadan kasar Sin a Birtaniya Liu Xiaoming, ya soki Birtaniya bisa yunkurin da take ci gaba da yi na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasarsa da yin zagon kasa ga dokarta ta tsaro, bayan Birtaniyar ta ce za ta bada shaidar zama dan kasa ga 'yan Hong Kong miliyan 3, a wani mataki na martani dangane da zartar da dokar tsaro da Beijing ta yi.

Lokaci ya yi da ya kamata Birtaniya ta fahimci cewa, yanzu yankin Hong Kong ba ya karkashinta. Hong Kong mallakin kasar Sin ne, kuma ita ke da iko da ita, ba Birtaniya ba. Duk wani hakki da ya kamata gwamnati ta sauke, yana wuyan kasar Sin ba Birtaniya ba. Birtaniya ta kan manta cewa yanzu ba lokacin mulkin mallaka ba ne da za ta rika yadda ta ga dama a kan Hong Kong.

Idan ba goyon rashin gakiya ba, mene ne laifin zartar da dokar tsaro? Tsaron muhimmin batu ne da tabbatar da shi ya rataya a wuyan gwamnati. Amma kuma a wannan gaba, sai ake ganin baiken kasar Sin don ta yi kokarin sauke daya daga cikin muhimman nauye-nauyen da suka rataya wuyanta. Wannan ya nuna a bayyane cewa, kasashen yamma na yin baki biyu dangane da kudurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duniya. Maimakon su goyi baya tare da jinjina matakan tsaro da ake dauka, sai suke kokarin yin zagon kasa tare da kawo cikas don kawo rarrabuwar kawuna da haifar da rikici a kasashen da ba nasu ba.

Kowacce kasa na da irin tsarin da ta zaba na tafiyar da harkokinta, wadanda suka dace da muradunta da na daukacin al'ummarta. Wannan dabi'a kuma, na daya daga cikin abubuwan da ya sa kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri har ta zama babbar kasa a duniya. Duba da cewa, ita ba ta zama 'yar amshin shata, ko kuma hakura da muradunta don farantawa wata ko wasu kasa. Har kullum, ta kan tsara manufofi da muradunta bisa halin da take ciki, kuma yadda za su dace da al'ummarta, wanda abu ne da ya kamata sauran kasashe su yi koyi da shi, maimakon suka.

Kamar yadda, Martin Jacques, fitaccen masanin nan na Birtaniya ya bayyana, ya kamata kasashen yamma su dauki alhakin rikicin dake wakana a HK. La'akari da goyon bayan da suke ba masu tada rikicin da kuma yadda suka dauki zafi kan matakin kasar Sin na zartar da dokar tsaro, mutum ba zai iya kaucewa tunanin cewa suna da hannu wajen kistawa da shirya rikicin ba tun fil azal.

Idan har da gaske ake ana son tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, to wajibi ne kasashe masu karfi su daina tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. Kamata ya yi su mara musu baya idan suka yanke hukuncin da bai sabawa doka ko kauce hanya ba, domin karfafa zaman lafiya a tsakanin al'umma.

An riga an fayyace dokar, inda aka nuna cewa, za ta mayar da hankali ne kan tsiraru masu aikata laifuffuka, sannan ta kare galibin mutanen yankin masu kiyaye doka da oda. Wannan ya dace da yanayin da Hong Kong ke ciki, la'akari da matsayinta na cibiyar hada-hadar kasuwanci, kuma mai samun baki akai- akai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China