Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tura dakaru na musamman 780 don murkushe 'yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar
2020-07-06 20:27:59        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar 'yan sandan kasar ta tura dakaru na musamman 780 don kawar da ayyukan 'yan bindiga da suke cin karensu babu babbaka a jihar Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Gwamnan jihar Zamfara wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta, ya ce tura dakarun zai kara karfafa tsaro da tabbacin jama'a kan gwamnatin jihar. Yana mai cewa, fashi da makami da satar mutane da sauran munanan ayyuka, sun zama ruwan dare a jihar a 'yan watannin nan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China