Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Darektan JKS ya jagoranci fitar da manoma daga kangin talauci ta hanyar kiwon dabobbi
2020-07-06 13:57:02        cri

Gundumar Gande ta jihar Guoluo ta kabilar Zang mai cin gashin kanta dake lardin Qinghai, ta taba yin matukar fama da talauci, garin Xielong da ke gundumar yana kan tudu dake da matukar sanyi, inda zaman rayuwar mazaunan wurin ke dogaro da yanayi saboda sha'anin kiwon dabobbi. A Watan Yulin shekarar 2017, Liu Yinzhou wani ma'aikacin kamfanin CRCC ya zama darektan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai kula da harkokin yaki da talauci a wannan kauye, a cikin shekaru 3 da suka gabata, a karkashin jagorancinsa, matalauta iyalai 93 sun fita daga kangin talauci.

Kauyen Xielong mai kabilar Zang na da iyalai 215, daga cikinsu 93 na fama da talauci, kuma shi ne kauye mafi fama da tsananin talauci daga cikin kauyuka 14 na gundumar Gande.

A shekarar 2017, ba da dadewa ba da Liu Yinzhou ya isa wannan kauye, ya yi nazari mai zurfi, ya gane cewa, gundumar na da fifiko matuka a fannin kiwon Yak.

A shekerar 2016 kuma, kamfanin CRCC ya zuba jarin kudin Sin Yuan fiye da dubu 500 a wurin don kafa sansanin sarrafa abincin dabbar yak mai fadin murabba'in mita dubu 190, bayan Liu Yinzhou ya isa wurin, ya habaka wannan sansani har fadinsa ya kai murabba'in mita 3,500,000, ban da wannan kuma, Liu Yinzhou da shugabannin garuruwa da gundumomi sun hada kai da shigar da wani kamfanin kiwon dabobbi don kiwon dabbar yak bisa kimiyya da fasaha, kuma suna sa ran a iya gudanar da sha'anin sarrafa naman yak nan gaba.

Ya zuwa yanzu, kauyen Xielong ya zuba jarin Yuan fiye da miliyan 1 a cikin wannan kamfani, kuma a ko wace shekara mazaunan suna samun riba.

A watan Afrilun bana, kauyen Xielong ya fita daga kangin talauci a hukumance, kana kuma, gundumar Gande ita ma ta janye jiki daga masu fama da talauci.

A wannan shekara kuma, saboda sayar da kayayyaki ta hanyar gabatar da kayayyaki ta bidiyo kai tsaye a kan Intanet ya samu karbuwa matuka a nan kasar Sin, Liu Yinzhou ya gwada wannan dabara don habaka hanyar kawar da talauci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China