Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kaddamar da matakan yaki da ambaliyar ruwa
2020-07-03 10:35:53        cri

Ma'aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Sin, ta sanar a jiya Alhamis cewa, kasar ta kaddamar da matakan gaggawa na IV na kandagarkin ambaliyar ruwa, yayin da aka shiga tsakiyar lokacin ambaliya a kasar.

Ma'aikatar ta ce hedkwatar yaki da ambaliyar ruwa da rage radadin fari, ta tura tawagogin ma'aikata zuwa yankunan Hunan da Hubei da Anhui, don jagorantar aikin rage radadin bala'in. Tana mai cewa, a halin yanzu aikin daidaita ambaliyar, da ceton gaggawa, da rage radadin bala'in ya shiga lokaci mai sarkakiya.

A jiya ne, a karon farko a wannan shekara, kogin Yangtze ya yi ambaliya, har ruwansa ya kwarara cikin babbar madatsar ruwa ta kasar Sin, inda cubic mita 50,000 na ruwa ke malala cikin ko wane dakika.

Yawan ruwa a tafkin Taihu, tafki na biyu mafi girma a kasar, shi ma ya zarce mizanin gargadi, yayin da matsakaicn mizanin ruwa da kasa da haka, a kogin Yangtze da tafkin Dongting da na Poyang sun dara mizanin da aka saba gani. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China