Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ware yuan miliyan 150 domin tunkarar ambaliyar ruwa
2020-07-01 10:57:05        cri

Ma'aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Sin (MEM) ta ce gwamnatin tsakiya ta kasar, ta ware yuan miliyan 150, kwatankwacin dala miliyan 21.2, domin ayyukan tunkarar ambaliyar ruwa da tallafi a lardunan kasar 3.

Ma'aikatar kudi da ma'aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar ne suka ware kudin ga lardunan Sichuan da Guizhou da Hunan, bayan gargadin ambaliyar ruwa a yankunan ya kai mataki na 4, wanda shi ne mataki na karshe a kasar.

Hukumar kula da ayyukan rage aukuwar annoba da ma'aikatar agajin gaggawa, sun kuma tura tawaga ta musammam zuwa yankunan da suka fi fuskantar ambaliyar ruwa a lardunan 3 da nufin gudanar da ayyukan rage radadin annoba.

Tun daga farkon watan Yuni, ambaliyar ruwa ta shafi kimanin mutane miliyan 12 a yankuna 13 na matakin lardi, a kudancin kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China