Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta cika shekaru 99 da kafuwa
2020-06-30 14:34:11        cri





Gobe Laraba 1 ga watan Yuli, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta cika shekaru 99 da kafuwa. Daga jam'iyyar da ke da mambobi sama da 50 kawai a farkon kafuwarta zuwa jam'iyyar da ta fi girma a duniya yanzu, shin yaya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin take ta ci gaba duk da matsalolin da ta fuskanta? Yaya kuma take rike tagomashinta a cikin shekaru kusan 100 da suka wuce?

A ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2017, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya kai ziyara biranen Shanghai da Jiaxing na kasar tare da sabbin zaunannun mambobin hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar, inda suka ziyarci wurin da aka gudanar da taron wakilan jam'iyyar karo na farko a birnin na Shanghai da kuma wani jan jirgin ruwa da ke birnin Jiaxing da aka sanar da kafuwar jam'iyyar, don waiwayen tarihin jam'iyyar da kuma alkawuran da aka dauka lokacin shiga jam'iyyar, lamarin da ya shaida niyyar sabbin shugabannin jam'iyyar.

Waiwaye adon tafiya, kome nisan tafiya, kada a manta da inda za a dosa. A biranen Shanghai da kuma Jiaxing, shugaba Xi Jinping ya sha bayyana muhimmancin "tuna baya", inda ya ce,"A rika tuna baya, ta haka za a cimma burin da aka sanya a gaba. Ainihin manufar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma burin da ta sanya a gaba shi ne jin inganta rayuwar al'ummar kasar, wadanda suke rika sa kaimin ci gaban 'yan jam'iyyar."

A shekarar 2020, ana fatan fitar da dukkanin mutanen da ke fama da talauci a yankunan karkara daga wannan matsala da suke ciki, wannan alkawari ne da jam'iyyar kwaminis ta kasar ta dauka wa jama'ar kasar. Duk da munanan illolin da annobar Covid-19 ta haifar ga tattalin arzikin kasar, amma shugaba Xi ya nanata cewa, "dole ne a cimma burin bisa lokacin da aka tsai da, babu ja da baya." Ya ce,"Mutanen zamaninmu na da wani buri, wato dole ne mu tallafa wa al'ummarmu, musamman na manoman kasar. Ba za a bar wani a baya ba a kokarinmu na wadatar da al'ummar kasar."

A yayin da annobar cutar Covid-19 ta barke, nan da nan jam'iyyar ta bayyana cewa, ya kamata a dora lafiyar al'umma a gaban kome. A game da wannan, shugaba Xi Jinping ya ce, "Al'umma ita ce a kan gaba, kuma rayukan al'umma sun fi komai muhimmanci, za mu yi duk mai yiwuwa wajen kare lafiyar al'umma."

A kokarin da ake yi na yaki da annobar, kasar Sin ta tara ma'aikatan lafiya da suka fi kwarewa da kuma na'urorin kiwon lafiya da suka fi inganci, kana ta hada karfin kowane bangare na kasar, don kare lafiyar al'ummar kasar.

To, amma me ya sa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin take iya yin duk mai yiwuwa domin kare lafiyar al'umma da kuma fitar da al'umma daga kangin talauci? Hakika kamar yadda shugaba Xi Jinping ya ce, "Jam'iyyarmu ba ta da wata moriya ta kanta da take neman cimmawa, kullum abin da ke gabanta shi ne moriyar al'umma." Ya ce, "Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samo tushenta ne daga jama'a, kuma tana tsayawa kan manufar dora al'umma a gaban kome, duk wani kalubale da muke fuskanta, duk abin da zai biyo baya, babu abin da zai sauya matsayarmu."

Tun bayan taron wakilan jam'iyyar kwaminis da aka gudanar karo na 18, shugaba Xi Jinping ya burge kasashen duniya bisa ga niyyarsa da kuma kwararan matakan da ya dauka na tafiyar da harkokin jam'iyyar da kuma yakar cin hanci da rashawa. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, yawan jami'an gwamnati da aka tsige daga mukamansu sun wuce na shekarun baya kwarai da gaske. A sa'i daya kuma, an gudanar da jerin ayyuka na inganta tsarin jam'iyyar. Shugaban Xi ya ce, "Abin da al'umma ke matukar kyama shi ne cin hanci da rashawa, kuma cin hanci shi ne babbar barazana da jam'iyyarmu ke fuskanta. Jam'iyyarmu ba za ta dora ba, illa dai mu kiyaye niyyarmu ta yaki da cin hanci da ci gaba da tsabtace jami'an gwamnati."

Farfadowar kasar Sin, na da alaka da ci gaban jam'iyyar kwaminis. Daga wata karamar jam'iyya a farkon kafuwarta zuwa jam'iyya mai karfi ta yanzu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai mulkin kasar da ke da al'umma biliyan 1.4, tana ta ci gaba duk da kalubalen da ta yi ta fuskanta.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China