Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kokarin raya sana'ar yawon bude ido a yankunan karkarar kasar Sin
2020-06-30 13:19:53        cri

Kauyen Yazha, yana garin Bajiao na gundumar Lintan dake yankin Gannan na kabilar Zang mai cin gashin kai, a lardin Gansu na kasar Sin. Bawan Allah Li Haifeng, shi ne darektan kwamitin kula da harkokin kauyen, wanda ya fara aikin a shekara ta 2014. A cewarsa, kauyen Yazha yana kan tsauni, wanda ke fama da matsalar zirga-zirga, abun da ya sa mazauna wurin ba su iya samun kudin shiga sosai, kana muhallin rayuwarsu ma ba shi da kyau.

A shekara ta 2015, gwamnatin wurin ta sake tsugunar da mazauna kauyen a wuraren dake kusa da hanyoyin mota.

A 'yan shekarun nan, gundumar Lintan tana himmatuwa wajen bunkasa sana'ar yawon bude ido a karkara domin taimakawa habakar tattalin arzikin wurin. Darektan Li yana kuma tunanin taimakawa mazauna wurin amfani da gidajensu don su zama wuraren yawon shakatawa, ta yadda zaman rayuwarsu zai iya inganta.

Sakamakon kokarin da Li yake yi, kawo yanzu akwai gidaje 25 a kauyen Yazha wadanda suka kebe wuraren zamansu don su zama na yawon bude ido. Haka kuma, gwamnati tana samar musu da rance ba tare da ruwa ba, gami da horo kan dabarun gudanar da kasuwanci.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China