Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara inganta tsarin ba da ilimin yara masu bukata ta musamman
2020-06-29 12:48:36        cri
Ma'aikatar ilimin kasar Sin, ta sha alwashin kara inganta dabarun ba da ilimi ga yara masu bukatu na musamman, a ajujuwa na kowa da kowa, don tabbatar da samar da ilimi ga daukacin yaran kasar.

Ma'aikatar wadda ta fitar da wani kundin bayani mai kunshe da wannan manufa, ta ce burin ta shi ne kawar da duk wani shamaki da ka iya hana yara masu nakasa samun damar yin karatu a ajujuwa na kowa da kowa, tare da kara inganta matsayin ilimin wannan aji na yara.

Har ila yau, karkashin manufar, za a yi cikakken amfani da rumbun tattara bayanan yara 'yan makarantar firamare da na midil, don tabbatar da cewa masu bukata ta musamman dake da hazakar koyon karatu, a tsakanin shekarun samun ilmin tilas, ba su kauracewa makarantar ba.

Game da batun ingancin ilimin kuwa, kundin ya jaddada muhimmancin daidaita abubuwan da ake koyawa dalibai da tsarin da ake bi don horas da dalibai, ta yadda za su dace da bukatun yara nakasassu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China