Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya za ta samar da guraben ayyukan yi miliyan 5 bayan COVID-19
2020-06-26 11:00:00        cri
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin samar da guraben aikin yi miliyan 5, bayan an gama yaki da COVID-19 a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.

Ministan kula da masana'antu da cinikayya da zuba jari na kasar Adeniyi Adebayo, ya ce daya daga cikin shirin gwamnatin na farfado da harkoki bayan COVID-19 shi ne, ceto kimanin ayyuka miliyan 1.4.

Ya ce kaso 10 daga cikin ayyukan da za a ceto suna bangaren bukatun musammam, sai kaso 40 a bangaren sana'o'in mata da kananan da matsakaitan sana'o'i.

Shirin na gwamnatin zai kuma ceto wasu karin ayyuka 300,000 a bangaren kanana da matsakaitan sana'o'i.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin Nijeriya ta tsara shirye-shirye da dama da suka mayar da hankali ga tsarukan gudanarwa da bibiya da nazari, domin tabbatar da aiwatar da shirin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China