Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
BOAD ya amince da ware dala miliyan 391 don gudanar da ayyukan raya yankunan yammacin Afirka
2020-06-26 10:34:24        cri
Bankin raya yammacin Afirka BOAD, ya ce daraktocinsa sun amince da ware kudaden da yawansu ya kai Francs biliyan 228, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 391, ga kungiyar raya tattalin arziki da hada hadar kudade ta yammacin Afirka WAEMU. Kudaden da ake fatan amfani da su wajen gudanar da ayyuka daban daban na raya sassan nahiyar.

Rahotanni na cewa, cikin wadannan kudade, za a yi amfani da Francs biliyan 128, wajen gudanar da ayyuka 8 a kasashen Mali, da Cote d'lvoire, da Nijar, da Togo, da Benin da Senegal. Kaza lika za a kashe Francs biliyan 100 wajen karfafa jarin cibiyoyin samar da rance na kungiyar WAEMU.

Wata sanarwa da aka fitar yayin taro na 117 na majalissar daraktocin bankin ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, daga birnin Lome helkwatar hukumar, bayan da aka amince a kashe wadannan kudade, ta ce ya zuwa yanzu, irin wadannan ayyuka na BOAD, sun lashe Francs tiriliyan 6.2.

Bankin BOAD cibiya ce ta hada hadar kudade mai mambobi 8, na kasashen kungiyar WAEMU, wato Benin, da Burkina Faso, da Cote d'lvoire, da Guinea Bissau. Sauran su ne Mali, Nijar, da Senegal da kuma Togo. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China