Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Huldar Sin da kasashen Turai bayan wucewar annobar Covid-19
2020-06-23 14:31:05        cri

 






Da daren jiya Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sabbin shugabannin kungiyar tarayyar Turai (EU) ta kafar bidiyo, shugabannin da suka hada da shugaban majalisar Turai Charles Michel, da shugabar hukumar zartaswar kungiyar Ursula von der Leyen, ganawar da ta kasance karo na biyar a tsakanin shugaba Xi Jinping da shugabannin kasashen waje, tun bayan da aka fara yaki da cutar Covid-19.

A ganawar da aka gudanar a daren jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana wa shugabannin kungiyar tarayyar Turai matsayar kasarsa. Yana mai cewa: Kasar Sin tana rungumar zaman lafiya a maimakon fin karfin wani, kuma kasar Sin dama ce a maimakon barazana, kuma kawa ce a maimakon abokiyar karawa. Ya ce, kamata ya yi Sin da Turai su martaba juna, tare da zurfafa fahimtar juna, su kuma yi kokarin neman cimma daidaito, a yayin da kuma suke amincewa wanzuwar sabanin ra'ayi a tsakaninsu. Sa'an nan, su yi kokarin habaka moriya ta bai daya a hadin gwiwarsu.

 

Su kuma a nasu bangaren, shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun bayyana cewa, Turai na son yin shawarwari da kasar Sin, don kara cimma daidaito a tsakaninsu.

A yayin da ake tsaka da yaki da cutar Covid-19 a duniya, shugabannin sassan biyu, sun kuma bayyana damuwarsu kan yanayin da duniya ke ciki. A game da wannan, shugaba Xi Jinping ya gabatar da cewa, kasancewar su manyan ginshikai biyu a duniya, wadanda ke da manyan kasuwanni da kuma wayewar kai, matsayin da sassan biyu suka dauka, da kuma hadin gwiwar da suke aiwatarwa na da muhimmiyar ma'ana, har ga duniya baki daya.

To, shin ko yaya Sin da Turai za su aiwatar da hadin gwiwarsu bayan da annobar Covid-19 ta wuce? A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya ce, ya kamata sassan biyu su yi kokarin gano damar hadin gwiwa a yayin da suke fuskantar matsalar. Ya ce, ya kamata Sin da Turai su kasance manyan ginshikai biyu na duniya, ta fuskar kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Annobar Covid-19 ka iya kara tsananta rikice-rikice da ake fuskanta a fadin duniya.

Ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma tarayyar Turai ta kasance kungiya mafi girma ta hadin kan kasashe masu arziki. Yadda sassan biyu suke ta kara mu'amala da juna a kan harkokin duniya, zai iya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya.

Shugaba ya kara da cewa, kamata ya yi Sin da Turai su kasance manyan kasuwanni biyu, na sa kaimin kiyaye ci gaba da wadata a duniya. A yayin da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara hedkwatar kungiyar tarayyar Turai. Ya ce, ya kamata Sin da Turai su zama injuna biyu na samar da karuwar tattalin arzikin duniya. Bayan abkuwar annobar, ya kamata "injunan biyu" su taka rawarsu yadda ya kamata, don sa kaimin farfado da tattalin arzikin duniya. A yayin ganawarsu, sassan biyu sun bayyana cewa, ya kamata su gaggauta shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari a tsakaninsu, don a daddale yarjejeniya cikin sauri.

Shugaba Xi Jinping ya ci gaba da cewa, Sin da Turai za su kasance ginshikai biyu, na kiyaye ra'ayin cudanyar bangarori da dama. Ya kuma jaddada cewa, duk da sauye-sauyen da suka faru a duniya, kasar Sin za ta kiyaye manufar nan ta cudanyar bangarori da dama, kuma za ta tsaya ga yin shawarwari da juna, wajen gudanar da harkokin duniya. A yayin ganawar, shugabannin kungiyar tarayyar Turai, su ma sun bayyana matsayinsu na kiyaye manufar.

Bana ake cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da kungiyar tarayyar Turai. A yayin ganawar su, shugaba Xi Jinping ya ce, yana son ci gaba da yin mu'amala da shugabannin biyu, don sa kaimi ga ajandar siyasa a tsakanin sassan biyu, da kuma ciyar da huldar da ke tsakaninsu gaba.

Shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa, duk nisan da ke tsakanin Sin da Turai, amma sassan na rayuwa ne a duniya daya. A lokacin da Sin da Turai ke cikin wani muhimmin lokaci na samun ci gabansu, dukkansu na fuskantar zarafi, da kalubalen da ba a taba gani ba. Kuma hadin kansu zai tabbatar da kyakkyawar makoma gare su. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China