2020-06-23 09:53:03 cri |
Wata tawagar jami'an kiwon lafiya wanda lardin Hunan da ke yankin tsakiyar kasar Sin ya zabe su sun riga sun koma gida bayan sun bada taimako a aikin yaki da annobar COVID-19 a kasashen Zimbabwe da Equatorial Guinea.
Hukumar lafiyar kasar Sin ne ta aike da tawagar kai tsaye zuwa kasar Zimbabwe tare da tallafin kayayyakin kiwon lafiya wanda gwamnatin lardin ta samar a ranar 11 ga watan Mayu, inda suka gudanar da aikin kula da lafiya a kasashen Afrika na tsawon wata guda.
Zhu Yimin, mataimakin daraktan hukumar lafiya na lardin Hunan, kana shugaban tawagar, ya ce sun ziyarci wasu cibiyoyin kiwon lafiya da na gwaje-gwaje a kasashen Zimbabwe da Equatorial Guinea domin yin musayar kwarewar da kasar Sin ta samu a yaki da annobar COVID-19.
A cewar Zhu, tawagar ta yi aikin hadin gwiwa da jami'an lafiyar kasashen game da aikin kula da majinyata da baiwa ma'aikatan lafiya na kasashen shawarwari dangane da aikin gwaje-gwaje domin inganta yanayin gwajin masu kamuwa da cutar. Tawagar ta kuma mika wasu rubutattun bayanan shawarwarin kwararru kan dabarun yin kandagarki da dakile yaduwar annobar. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China