Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labarin Furfesa Xie Zheng a Afirka
2020-06-22 19:03:35        cri

A yammacin ranar 4 ga watan Yuni, Furfesa Xie Zheng, mataimakiyar shugaban sashen ilmin kiwon lafiyar al'ummun duniya ta Jami'ar Peking ta ce, tana son yin dan barci, amma daga baya ba ta farka daga barcin ba. A duk tsawon rayuwarta, Furfesa Xie mai shekaru 41 da haihuwa ta dukufa kan aikin raya harkokin kiwon lafiyar jama'a dake da nasaba da kasashen Afirka.

A matsayinta na wata kwararriyar ilmin kiwon lafiyar jama'a, Furfesa Xie ta sa kaimi ga aikin kafa sansanin farko na kasar Sin ta fuskar kiwon lafiyar jama'a a ketare a shekarar 2014, yayin ta ba da gudummawa wajen aikin kafa cibiyar nazari da aikin koyarwa ta kwalejin kiwon lafiyar jama'a dake Jami'ar Peking a kasar Malawi a shekarar 2017.

Bayan an kafa cibiyar, Jami'ar Peking ta hada gwiwa tare da kwalejojin likitanci da hukumomin likitanci na kasar Malawi a fannonin kiwon lafiyar duniya, lafiyar yara da mata, cutuka masu yaduwa, manufofin kiwon lafiya da dai sauransu, baya ga tura malamai da dalibai zuwa kasar sau da yawa don nazarin ilmin likitanci. Furfesa Xie Zheng ta taba zuwa Malawi sau da dama, inda ita da dalibanta suka yi mu'amala tare da mazauna wurin wajen yin nazari, a kokarin horar da kwararru a fannin kiwon lafiyar duniya da ma warware matsalolin kiwon lafiya da ke damun mazauna wurin.

Furfesa Zheng Zhijie, shugaban sashen ilmin kiwon lafiyar duniya na Jami'ar Peking ya tuna da cewa, "Madam Xie Zheng na iya mu'amala da al'ummar Malawi yadda ya kamata, yadda ta fahimci harkokin Afirka da al'adun wurin da ma yanayin zamantakewar al'ummar wurin ya burge mu kwarai da gaske".

Yayin da ake raya cibiyar nazarin a Malawi, Furfesa Xie ta ganewa idanunta kan yadda cutar Malariya ke damun Malawi, Comores da dai sauran kasashen Afirka, yanayin kiwon lafiya maras kyau ma wurin kuwa ya kada ta sosai. Don haka yadda za a taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da malariya ya zama daya daga cikin fannonin da suka fi jawo hankalin Xie Zheng, koda yake batun ba shi da nasaba da nazarinta kai tsaye. "Malariya ta haddasa mutuwar dimbin yaran Afirka, kowane karon da na ga hakan, ina ganin cewa, ya kamata mu bayar da gudummawarmu." Xie ta yi wannan tsokaci, tare da fara yin la'akari da yadda za a yi amfani da Artemisinin wajen taimakawa al'ummomin kasashe masu tasowa.

Madam Xie Zheng ita ma wata manazarciya ce mai jin kai. Ta taba rubuta cewa, "Na sani, yayin da nake farantawa mutane rai, ya kamata in shirya sadaukar da kaina a ko da yaushe."

Xie ta taba ziyartar wurare daban daban na Afirka, kamar ta taba zuwa asibitin Jinjia na Uganda da asibitin sada zumunta na Sin da Uganda don tattaunawa da marasa lafiya da ma'aikatan jinya. Ta taba zuwa kasar Comores don tantance shirin yaki da cutar malariya da Sin ke gudanarwa a kasar, da ma raya aikin kwasa-kwasai kan kandagarkin cutar.

Bugu da kari kuma, Madam Xie ta dukufa wajen nazari kan yadda Sin ta sa kami ga kawar da malariya a duk fadin duniya, lamarin da ya jawo hankalin sashen yaki da cutar Malariya na hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO. A watan Yunin shekarar 2018, WHO ta dauketa a matsayin jami'ar fasaha wajen sa hannu cikin aikin shawo kan cutar malariya na duniya.

A watan Yunin shekarar 2019, Xie Zheng ta kira taron karawa juna sani kan Artemisinin a Beijing, bisa aniyar tattaunawa kan yadda maganin yaki da malariya da masana'antun samar da magunguna na Sin zai samu amincewa daga WHO. Xie ta gayyaci Pedro Alonso, shugaban sashen tsara shirin yaki da cutar malariya na duniya na WHO da ma kwararru masu nazarin cutar na gida da na waje wajen halartar taron, a kokarin yada Artemisinin a duk fadin duniya, ta yadda zai amfana wa masu fama da cutar a wurare daban daban. Amma a wancan lokaci, ta riga ta kamu da cutar sankara.

Domin share fagen babban taron, Madam Xie ta yi fama da aiki har zuwa daren jajibirin ranar bude taron, lamarin da yasa ba ta ji lafiya sosai ba a safiyar ranar, har ma ma'aunin hawan jininta ya kai 150. Bayan shan magani, ta ci gaba da shiga tattaunawar wancan rana, lamarin da ya sa kowa ya dame ta sosai.

Kwarewar aikin Madam Xie ta samu jinjinawa da girmamawa daga takwarorinta na kasa da kasa. Da jin labarin rasuwarta, Pedro Alonso, shugaban sashen tsara shirin yaki da cutar malariya ta duniya na WHO shi ma ya aiko da sakon ta'aziyya, inda ya bayyana cewa, "Furfesa Xie Zheng ta kara azama ga hadin gwiwar da ke tsakanin WHO da kasar Sin, tare da taimaka wa duniya wajen fahimtar amfanin Sin a fannin samar da taimako don yaki da cutar malariya."

Haka zakila ma, uwargidan shugaban kasar Malawi ta aiko da sakon ta'aziyya, don nuna bakin ciki da kaduwa da ta ji bayan samun labarin rasuwar wannan aminiyarta kuma manazarciya mafi kwarewa.

A idanun dalibanta da ma abokan aikinta, ko da yaushe Madam Xie Zheng tana gudanar da aiki a tsanake, idan aikin bai samu gamsuwa daga sauran mutane ba, to ba za ta ji dadi ba. Furfesa Liu Peilong, tsohon shugaban sashen kiwon lafiyar duniya na Jami'ar Peking ya furta cewa, "Xie Zheng ta nuna matukar sha'awa ga aikin kiwon lafiyar duniya, ta kuma yi nazari sosai a wannan fanni. Ilmin da take da shi yana da yawa idan an kwatanta da sauran masanan da shekarunsu suka yi daidai da nata. Rasuwarta ta sa na rasa wata aminiya a fannin ilmi."

Madam Xie Zheng wata mai sa ran alheri kan komai ce. Har ma a lokacin da take kwance a asibiti don yaki da cutar sankara, ta yi kokarin kiyaye kyakkyawan hali, tana motsa jiki a ko wace rana, da cin abinci mai gina jiki, har ma tana rike da wata karamar kwallo a hannunta ko da yaushe don mota jiki. Har ma a karon karshen da aka kai ta asibiti sakamakon tsanantar cutar sankara, Xie Zheng ta saya wa kanta wani dogon fatari, domin sanya shi yayin da aka sallame ta daga asibitin.

A ofishin Madam Xie Zheng, wata taswirar zirga-zirga ta kasar Malawi da ke jikin bango ta jawo hankalin mutane sosai. A gaban taswirar, ana iya ganin takardun bayani, takardar lambobin waya, takardar kalmomin Sinanci da Faransanci da dai sauransu.

Abokan aikinta da ma dalibanta sun ce, har yanzu suna ganin cewa, Furfesa Xie Zheng ba ta bar su ba, sai dai ta sake zuwa nahiyar Afirka.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China