Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu karuwar jarin waje na kai tsaye
2020-06-19 13:03:06        cri

Ma'aikatar cinikayya ta Sin, ta ce babban yankin kasar ya samu karin jarin waje na kai tsaye ko FDI a takaice, da karuwa kaso 7.5 bisa dari a shekara, inda a watan Mayu, yawan sa ya kai kudin Sin yuan biliyan 68.63.

Da yake tabbatar da hakan, yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce wannan adadi ya yi daidai da dalar Amurka biliyan 9.87, karuwar da ta kai kaso 4.2 bisa dari a shekara guda.

Jami'in ya kara da cewa, tsakanin watannin Janairu da Mayu, jimillar FDI na kasar Sin ya kai yuan biliyan 355.18, wanda ya yi kasa da kaso 3.8 bisa dari a shekara guda, daidai da ragin kaso 7 bisa dari idan an kwatanta da na watani ukun farkon shekarar.

Tsakanin wannan lokaci, karuwar FDI cikin harkokin manyan masana'antu na zamani ya daga da kaso 2 bisa dari, inda harkokin sadarwa ya samu karuwar kaso 42.3 bisa dari, kana na cinikayya ta na'urori ya samu karuwar kaso 67.9 bisa dari.

Bugu da kari, zuba jari a fanni FDI daga kasashe mambobi kungiyar kudu maso gabashin Asiya, ya karu da kaso 10.1 bisa dari a shekara guda, yayin da jarin na FDI, daga kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, ya daga da kaso 6 bisa dari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China