Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Masar ya halarci taron kolin Sin da Afrika kan yaki da COVID-19
2020-06-19 10:16:32        cri

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a ranar Laraba ya halarci taron kolin Sin da Afrika, game da hadin gwiwarsu a fannin yaki da annobar COVID-19, kamar yadda fadar shugaban kasar Masar ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Taron kolin, wanda aka gudanar ta kafar bidiyo, ya samu halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin kasashen Afrika da dama.

Taron nan, a cewar shugaba Sisi, zai taimaka wajen daga matsayin kyakkyawar dangantakar siyasa dake tsakanin Afrika da Sin, da kuma cika burin da Afrika ke da shi na cigaba da dakile tasirin annobar COVID-19, karkashin hadin gwiwa da kasashen duniya kamar kasar Sin, inji sanarwar.

Shugaban na Masar ya jaddada taron kolin na Sin da Afrika kan yaki da annobar COVID-19 da cewa an shirya taron ne domin nuna goyon baya a siyasance, da yin hadin gwiwa, da nufin cimma moriyar bangarorin biyu.

Sisi ya kuma yabawa salon da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen dakile annobar, inda ya jaddada bukatar koyon darasi daga kasashen da suka samu manyan nasarorin dakile yaduwar annobar ta COVID-19. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China