![]() |
|
2020-06-15 21:20:21 cri |
Kakakin ya bayyana hakan ne, a yayin taron manema labaru da aka yi a yau Litinin, inda ya kara bayyana cewa, kwamitin lafiya na kasar Sin ne ya kafa tawagogin, kuma gwamnatin birnin Chongqing, da ta yankin musamman na Macau, su ne suka zabi kwararru na tawagogin.
Baya ga haka, kakakin ya ce, kwararrun kasar Sin sun kuma mika wa ma'aikatar kiwon lafiya ta Algeria da ta Sudan, takardar da ta shafi shawarwarinsu kan ayyukan dakile annobar COVID-19 a wurin, da harsuna masu dama, don taimakawa hukumomin da batun ya shafa na kasashen biyu, wajen kara kyautata matakan tinkarar annobar, da kara karfinsu na ba da jinya, da kuma karfafa ayyukan dakile annobar, da ayyukan ceto bayan da aka soma farfado da aiki, shawarwarin da suka samu amincewa daga kasashen biyu. (Bilkisu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China