Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Prof. Emakoji Ayikoye: Ya kamata gwamnatin Amurka ta daidaita matsalar nuna wariyar launin fata
2020-06-16 14:06:56        cri


A cikin shirinmu na wannan mako, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da wani dan Najeriya mai suna Prof. Emakoji Ayikoye, malami ne dake koyar da ilimin kasuwanci ta fasahar sadarwa wato business information system a jami'ar City University dake birnin New York na Amurka. Prof. Emakoji, wanda ya shafe shekaru 20 yana karatu da aiki a Amurka, ya bayyana ra'ayinsa kan yadda gwamnatin Amurka take daukar matakan dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, inda kuma a cewarsa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka abin koyi ne ga duk duniya baki daya.

Game da matsalar nuna wariyar launin fata kuwa, wadda ta jima tana addabar Amurka, Prof. Emakoji Ayikoye ya bayyana yanayin da shi kansa da sauran bakaken fata suke ciki a wurin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China