![]() |
|
2020-06-14 16:42:11 cri |
Jimillar mutanen da annobar ta hallaka ya kai 6,040, yayin da mutane 102,846 sun warke daga cutar, kamar yadda alkaluman baya bayan nan na hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta bayyana.
Kasashen Afrika da annobar COVID-19 tafi yin kamari sun hada da Afrika ta kudu, Masar, Morocco, Djibouti, Najeriya, da Algeria, kamar yadda hukumar lafiyar ta AU ta sanar.
Baya ga kasashen 43 dake karkashin dokar tsaurara rufe kan iyakokinsu, Afrika CDC ta kara da cewa, an kafa dokar hana fita da dare a kasashen Afrika 35 a kokarin dakile yaduwar annobar.
A cewar Afrika CDC, dukkan kasashen Afrika 54 suna aiwatar da dokar takaita taruwar jama'a, kana wasu kasashen nahiyar 38 sun kafa dokar rufe makarantu a fadin kasashen, da kafa dokar kayyade ziyartar gidajen yari da asibitoci a kasashen Afrika 20.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China