2020-06-11 09:14:53 cri |
A kalla mutane 81 aka kasha, sannan an yi garkuwa da wasu mutane 7 a lokacin da wasu mahara da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kaddamar da hari a wani kauye dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Gwamnan jihar Babagana Zulum, ya fadawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, an kuma raunata mutane 13 a lokacin da maharan suka afkawa kauyen Faduma Koloram dake karamar hukumar Gubio a jihar Borno ranar Talata.
A cewar gwamna Zulum, dagacin kauyen yana daga cikin mutanen da mayakan wadanda suka je kauyen a kan babura suka yi garkuwa da su.
Harin na ranar Talata shi ne hari na uku da aka kaddamar a kauyen cikin kasa da wata guda, a cewar gwamnan wanda ya jagoranci jami'an gwamnatin jihar zuwa wajen da lamarin ya afku domin duba irin barnar da mayakan na Boko Haram suka haddasa.
Maharan sun kone gidaje masu yawa, sannan sun sace daruruwan shanu.
Zulum ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa jami'an tsaro domin ceto rayukan al'umma da dukiyoyin mazauna yankunan.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China