![]() |
|
2020-06-08 20:11:34 cri |
Ganin wadannan shaidu da ba za a iya musunta ba, wajibi ne 'yan siyasan kasar Amurka da suka yi surutun banza kuma suna yunkurin shafa wa kasar Sin kashin kaji su daina yin karya, su rufe bakinsu.
Bayan barkewar annobar ta COVID-19, kasar Sin ta dakile da kuma kangadarkin annobar ba tare da rufa-rufa ba, ta sauke nauyi bisa wuyanta yadda ya kamata. Ba ta boye kome wajen yaki da annobar ba. Matakan da ta dauka sun dace da zamani da tarihi.
Kasar Sin, wadda ta sha wahalhalun da annobar ta haddasa mata, ita kasa ce dake ba da gudummawa wajen hana yaduwar annobar a duniya. A don haka, kamata ya yi a yiwa kasar Sin adalci, a maimakon sukar ta.
Kamar yadda takardar bayanin ta fada, dole ne kasashen duniya su kara hada kansu yayin da suke fuskantar wannan abokin gaba na bai daya wato kwayar cutar COVID-19, su daina kallon duniya bisa ra'ayoyinsu, su daina nuna girman kai, su bar son kai da dora wa wasu laifi, kana su daina ci gaba da shafa wa wasu kashin kaji da sanya siyasa kan annobar.
Wadancan 'yan siyasan Amurka da suka sha yin karya kuma ba sa tunanin kalaman dake fita daga bakunansu, ya kamata su rufe bakinsu, su kara taimaka wa jama'arsu wajen rage radadin annobar. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China