Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar Jami'an Lafiya Dake Taimakawa Zimbabwe: Yakar Cutar COVID-19 A Cikin Mawuyacin Hali
2020-06-04 14:47:19        cri

Ran 11 zuwa 25 ga watan Mayu da ya gabata, Sin ta tura tawagar ma'aikatan lafiya zuwa Zimbabwe don taimakawa kasar wajen yakar cutar COVID-19, da more dabaru da fasahohinta na yaki da cutar, da horar da masu aikin jiyya na wurin, da ma baiwa kasar gudummawar kayayyakin kandagarki. Hukumar kiwo lafiya ta lardin Hunan na kasar Sin ce ta tura wannan tawaga mai masana 12, wadanda suka kware matuka a fannin numfashi, da shawo kan cututtuka masu yaduwa wadanda ke da tsanani, da ba da kulawa ga majiyyata da sauransu. Tawagar ta samu karbuwa da kuma yabo matuka daga gwamnati da jama'ar kasar Zimbabwe.

Masu aikin jiyya a Zimbabwe sun samu horo sosai a baya, kuma kasar tana kan gaba a nahiyar Afirka a fannin amfani da tsarin kimiyya wajen yin jiyya, amma saboda koma bayan tattalin arziki a shekarun baya-bayan nan, babu likitoci da magunguna masu kyau a asibitocin gwamnati, kana wasu na'urori sun lalace saboda rashin kulawa. Wata matsalar ita ce a wani lokaci babu ruwa da wutar lantarki a wani asibiti dake Harare, fadar mulkin kasar, wanda aka mai da shi asibitin kula da masu kamuwa da cutar COVID-19. A sa'i daya kuma, albashin masu aikin jiyya bai taka kara ya karya ba a kasar, abin da ya sa masu aikin jiyya a kasar, ba su mayar da hankali sosai kan aikinsu. Sa'an nan barkewar cutar COVID-19 cikin gaggawa, ta illata tsarin kiwo lafiyar kasar, wanda a baya ma ba shi da kyau.

Tawagar masana ilimin kiwon lafiya ta kasar Sin ta yi mu'ammala sosai da masu aikin jiyya a wurin, inda kokarin aiki da kishi da likitocin kasar suka nuna suka burge masanan kasar Sin sosai, kuma masana Sinawa sun damu sosai kan na'urori marasa inganci da ake samu cikin asibitin. Hakan ya sa, tawagar ta ba da shawarwari da suka dace da halin da wurin ke ciki, kana ta samarwa hukumomin jiyya kayayyakin kandagarki kyauta don taimakawa masu aikin jiyya na wurin, ta yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar. Ga abin da wasu masanan suka bayyana game da tsarin aikinsu lokacin da suke kasar Zimbabwe.

"Sunana Zhang Di, mataimakin farfesa a sashin gwaje-gwaje na asibitin Xiangya na 3 na jami'ar kudu maso tsakiya ta kasar Sin. Sa'an nan yau ranar 12 ce ga watan Mayu na shekarar 2020. Da sassafe za mu iya ganin cewa akwai motoci da dama dake gudu a kan hanyoyi. Hakan ya nuna wannan kasa na kokarin dawo da harkokin rayuwar yau da kullum yayin da take kokarin yakar cutar COVID-19. Yawancin mutane na sanye da marufin baki da hanci, abin da ya nuna cewa, Zimbabwe na daukar matakin da ya dace na kandagarkin cutar. Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun da matarsa suna bayyana mana kokarin da gwamnatin kasar ke yi don yakar cutar, kuma sun gaya mana cewa, kasar na fuskantar matsaloli da dama. Muna ganin cewa, wadannan matsaloli sun yi kama da matsalar da kasarmu ke fuskanta lokacin da aka gano wannan cutar, wato karancin kayayyakin kandagarki, da nau'urorin gwaji, da kuma matakan jiyya masu amfani. Abin da muka sanya a gaba yanzu, shi ne yadda za mu taimaka musu gwargwadon karfinmu."

"Sunana Wang Wenlong, mataimakin farfesa a sashin gwaje-gwaje na asibiti na 2 na jami'ar kudu maso tsakiya. Yau rana ce ta 16 ga watan Mayu na shekarar 2020. Ina ta tunani a wadannan kwanaki, kan cewar me ya sa ake raina aikin likitanci a kasar Zimbabwe? A ganina, gwamnatin kasar ba ta mutunta masu aikin jiyya, da samar musu tabbacin zaman rayuwa ba. Idan masu aikin jiyya suna fadi tashi don samun abinci, hakika, ba za su iya mayar da hankali wajen kula da maras lafiya ba. Saboda yawancin mutane na ganin cewa, akwai lokacin da za a sadaukar da kai, amma ba za a iya yin haka duk tsawo ransa ba. Yawan kudin shigar da 'yan kasar ke samu a wata, dala 20 ne kawai, amma kudin gwajin cutar zai kai dala 25, don haka fararen hula kusan ba wanda ke iya biya wannan kudi. Saboda haka, aiki mafi muhimmanci a gabansu shi ne hana yaduwar cutar a maimakon ba da jiyya, wato dakile asalin yaduwar cutar. Matakin da Zimbabwe ke dauka yanzu na killacewa ya dace da halin da ake ciki, a ganina, idan an gudanar da wadannan mataki yadda ya kamata, ana iya hana yaduwar cutar, kuma mataki ne da ba ya bukatar kashe kudi masu yawa."

"Sunana Deng Zhihong, ni ce darektar cibiyar kandagarkin cututtuka na lardin Hunan na kasar Sin. Yayin da nake mu'ammala da takwarorina na Zimbabwe, na fahimci cewa, kasar ta dauki manufofin da suka dace, kuma suna da tunani mai kyau da kokarin tabbatar da matakan da suka dauka, sai dai wata babbar matsalar da kasar ke fuskanta ita ce karancin kudade. Ko da yake kasar ta kebe asibitoci 70 don killace da ba da jiyya ga wadanda suka kamu da cutar, amma a rangadin da muka yi a wadannan kwanaki, abin da muka gani shi ne, babu wani asibitin da aka gyara tsarinsa sosai don biyan bukatar dakile cutar COVID-19, saboda babu kudi. Idan an samu barkewar cutar sosai a kasar, to, yaya za su yi. Likitocin kasar su ma sun fahimci babban kalubalen da suke fuskantar na rashin samun kayayyakin ba da jiyya, saboda haka sun fi mai da hankali kan matakan kandagarki. A matsayinmu na masana a wannan fanni, za mu iya warware matsalar kimiyya ne kawai, ba mu da karfin warware matsalar tattalin arziki. Don haka, muna fatan gwamnatin Zimbabwe za ta mai da hankali matuka kan hana shigo da kwayar cutar daga ketare, da dakile yaduwar cutar tsakanin unguwanni. "(Mai fassarawa: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China