Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar jami'an lafiya ta kasar Sin ta gabatar da dabarun yaki da COVID-19 ga kwamitin kula da lafiya na Sudan
2020-06-02 09:23:58        cri
Tawagar masana kiwon lafiya ta kasar Sin, ta gana a jiya, da kwamitin ayyukan lafiya na gaggawa na kasar Sudan, domin gabatar da dabarun yaki da COVID-19.

Wata sanarwar da mamban kwamitin, Hiba Ahmed ya fitar, ta ce tawagar ta kasar Sin, ta yi rangadi don nazarin ainihin yanayi da ake ciki da kalubalen da kasar ke fuskanta dangane da yaki da cutar.

A nasa bangaren, Jakadan kasar Sin a Sudan, Ma Xinmin, ya jaddada ci gaba da hadin gwiwa tsakanin Sin da Sudan wajen tunkarar COVID-19.

Ya ce kasar Sin za ta taimakawa kasar ta Sudan iya karfinta, ta hanyar gabatar da dabaru da gogewarta wajen sa ido da dakile cutar COVID-19.

Tawagar jami'an lafiyar ta isa Khartoum, babban birnin kasar Sudan ne a ranar Alhamis daga kasar Algeria, bayan ta kammala aikin makonni 2 a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China